Jarabarsa tayi yawa, a taimaka min a raba mu - Matar aure a gaban kotu

Jarabarsa tayi yawa, a taimaka min a raba mu - Matar aure a gaban kotu

- Mata ta kai karar mijin ta kotun magistare a Zimbabwe a kan bala'in sha'awarsa

- Inda tace likitoci sun shawarce ta da ta rage saduwa saboda ciwon da hakan ya haifar mata

- Mijin ya nuna takaicinsa saboda fallasa sirrin gidansu da matar tayi a idon duniya

Kotu ta amince da bukatar sakin wata mata 'yar kasar Zimbabwe a kan korafin cewa mijinta ya cika son jima'i.

Matar mai shekaru 42 ta nemi kotu da ta rabata da mijinta saboda sha'awarsa tayi yawa, kamar yadda gidan jaridar Lusaka Times ta ruwaito.

Matar mai yara biyu ta gaji da yawan jima'in da mijinta ke nemanta dashi, duk da likitoci sun shawarce ta da ta rage saduwa saboda ciwon da ke addabarta sakamakon yawon saduwa da miji.

A bangaren mijin, ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda matarsa ta fallasa matsalarsa ta sha'awa a idon duniya.

Bayan ji daga bakunansu, alkalin kotun ya amince da sakin matar, inda ya shawarci mutumin mai yara 11 da ya gyara rayuwar yaransa 11, maimakon mayar da hankali a kan jima'i da shaye-shaye.

KU KARANTA: Bidiyon dattijuwa daga Sokoto tana magana da yaren Ibo tiryan-tiryan babu kuskure

Jarabarsa tayi yawa, a taimaka min a raba mu - Matar aure a gaban kotu
Jarabarsa tayi yawa, a taimaka min a raba mu - Matar aure a gaban kotu. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Sojan Najeriya ya zane budurwa a kan shigar banza, ya aske ladabtar da matashi saboda askin kansa

A wani labari na daban, Augustine Yiga, shararren faston nan na Uganda ya mutu, Jaridar The nation ta wallafa.

Faston ya rasu ne bayan watanni 5 da kama shi da laifin yayata cewa Coronavirus zazzabi ne wanda dama aka dade ana yinsa.

Faston cocin Revival da ke Kawaala, a Kampala, wanda aka fi sani da Abizaayo, ya rasu ne a ranar 26 ga watan Oktoba, a asibitin Nsambya inda aka kwantar dashi sakamakon fama da ciwon hanta.

An kawo gawarsa cocin a ranar Asabar, 31 ga watan Oktoba da rana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng