Musulmi sun cigaba da zanga-zanga kan ɓatanci da aka yi ga Manzon Allah

Musulmi sun cigaba da zanga-zanga kan ɓatanci da aka yi ga Manzon Allah

- Masu zanga zanga na bukatar a daina siyan kayayyakin Faransa saboda batancin da suka yi wa annabi Muhammad

- Wata jam'iyyar siyasa ta musulmi ta bukaci a tsawaita zanga zangar zuwa wani satin

- Ana gangami a tsohon birnin Jerusalem, masallacin Kudus saboda batancin da Faransa tayi wa Annabi Muhammad

An cigaba da zanga-zanga, ranar Juma'a, a wasu ƙasashen Musulmi don nuna fushi kan kalaman shugaban Faransa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

An cigaba da zanga-zanga bayan sallar Juma'a a wurare daban-daban a zirin Gaza inda kungiyar Hamas ta bukaci masu zanga-zangar su hadu a sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia don cigaba da nuna fushin su kan batun.

Fathi Hammad, shugaba a ƙungiyar Hamas daga Jabalia ya yi kira ga wadanda suka fito tattalin su hada kai don tunkaro abinda ya kira "cin zarafi" ga Annabi Muhammad.

Musulmi sun cigaba da zanga-zanga kan ɓatanci ga Manzon Allah
Musulmi sun cigaba da zanga-zanga kan ɓatanci ga Manzon Allah. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: An kashe 'yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji - DHQ

Ana kuma gudanar da wani gangami bayan salloli a wajen masallacin Kudus a tsohon birnin Jerusalem, in ake kirarin "labbaika ya Muhammad" da kuma "kasar da Muhammad ya jagoranta bazata durkushe ba."

Zanga zanga ta kuma balle a kudancin Asia, inda dubban mutane mutane a Afghanistan da Pakistan suka shiga zanga zangar.

An gudanar da gangami a manyen biranen Pakistan, inda masu zanga zangar suke kirarin kin jinin Faransa, Kuna hotunan Shugaban Faransa Macron da kuma bukatar a dawo da jakadan Pakistan da ke Faransa.

Jamiat Ulama-e-Islam, babbar jam'iyyar siyasa ta addini, sunyi kira da aci gaba da zanga zangar zuwa wani satin.

Pakistan, kasar da ke da yawan da ya kai mutane miliyan 220 wanda mafi yawansu musulmi ne, sun gudanar da wata mummunar zanga zanga a shekarun baya saboda wani fim da aka dora a YouTube ana zagin Annabi Muhammad.

Sai dai, shaidun gani da ido sunce mutum 2,000 sun shiga gangamin a babban birnin Afghanistan Kabul, kuma daruruwa suna yi a yammancin Herat.

KU KARANTA: Duka ba kama suna: Hadimin Ganduje, Yakasai, ya sake caccakar mahukunta bayan mayar da shi kujerarsa

Masu zanga zangar suna kuma bukatar a daina siyan kayayyakin Faransa kan zanen barkwanci.

A baya bayan nan, an sarewa wani Malamin Faransa kai a tsakiyar Paris bayan ya nunawa dalibai zanen a wani darasi akan yancin fadin albarkacin baki.

A wani labarin, rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe yan ta'adda 22 lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari sansanin sojoji da ke Damboa, Jihar Borno.

Jami'in yada Labaran hukumar sojin, Manjo Janar John Enenche, ya ce maharan sun sha luguden wuta daga jami'an sojoji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164