An budewa musulmi masallaci na farko a Athens

An budewa musulmi masallaci na farko a Athens

- An kai ruwa rana kafin a kai ga bude masallaci na farko a babban birnin Greek Athens

- An gudanar da Sallah ta farko karkashin dokokin kariya daga cutar korona kuma ana tsammanin babban shagali bayan wucewar annobar

- Musulmi dubu goma ne ke zaune a kasar Greek cikin su akwai ma'aikata da yan gudun hijira

An bude masallaci a babban birnin Greek, Athens bayan shekaru 14 ana dambarwa, wata majiya ta kusa ta wallafa ranar Talata.

An gudanar da sallah ta farko a masallacin karkashin dokokin kariya daga cutar korona da yammacin Litinin cikin tsanaki, kuma mutane kaɗan ne suka halarci sallar.

Ana tsammanin babban shagali bayan wucewar annobar ta korona.

Bude masallacin ya nuna tsantsar dimokradiyya, da yancin gudanar da addini, an jiyo sakataren harkokin addinai, Giorgos Kalantzis yana fada kamar yadda jaridar Kathimerini ta ruwaito.

An budewa musulmi masallaci na farko a Athens
An budewa musulmi masallaci na farko a Athens. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An bindige malamin coci a Faransa

Yahudawan Greek ne dai suka jinkirta bude masallacin tun a shekarar 1979.

An dauki shekaru duk da sahalewar da gwamnati ta yi a shekarar 2006.

Limamin farko wani da aka haifa a Morocco, dan asalin kasar Greek Zaki Mohammed, Mohammed wanda ya karanci lissafi da harkokin addinai yana jin yaren Larabci, Girka da kuma Faransanci.

Kaso 97 cikin 100 na yan Kasar Greek dai Yahudawan kiristoci ne.

KU KARANTA: 2023: Kungiya ta yi barazanar yin ƙarar El-Rufai a kotu idan ya ki fitowa takarar shugaban kasa

Sai dai, duk da haka akwai musulmi kalilan da suke iyakar kasar da Turkiyya kuma ma'aikata da yan gudun hijira dubu goma da suke zaune a kasar.

A wani labarin, Aƙalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru a yammacin ranar Asabar a kasuwar Akungba ta Jihar Ondo.

An ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wata trela da ƙwace wa direban ta kutsa cikin kasuwar Akungba ta take mutum 10 har lahira tare da raunata wasu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel