An bindige malamin coci a Faransa
- Wani mutum ya harbi malamin coci a Faransa a yayin da ya ke kokarin rufe cocinsa a ranar Asabar
- Masu bada agajin gaggawa sun halarci wurin suna kokarin ceto ran malamin a yayin da wanda ya yi harbin ya tsere
- Farai ministan kasar Jean Castex ya isa wurin da abin ya faru inda ya shaidawa manema labarai cewa ba za su bari irin wannan harin ya 'karya musu gwiwa ba'
Wani da ya kai hari da bindiga ya tsere bayan ya harbi wani malamin cocin kibɗawa a birnin Lyon da ke kasar Faransa kamar a ranar Asabar.
Ya harbi malamin ne a cocin Église Greek Orthodox da ke Jean-Macé inda ya bar shi rai a hannun Allah.
Jami'ai masu bada agajin gaggawa sun isa wurin don kai masa dauki sannan an datse hanyar shige da fice a wurin.
BFM TV ta ruwaito cewa wani mutum shi daya dauke da bindiga ne ya harbi malamin cocin a yayin da ya ke kokarin rufe cocinsa a cewar 'yan sanda.
Ana kyautata zaton har yanzu dan bindigan yana nan ba a kamo shi ba.
DUBA WANNAN: Hotuna: An kashe 'yan ta'adda 22 yayin da suke kai hari sansanin sojoji - DHQ
Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Gérald Darmanin ya umurci mutane su guji zuwa wurin kuma ya ce shi da Farai Minista Jean Castex da Shugaba Emmanuel Macron za su hadu a wurin.
Sai dai Farai Minista Castex tuni ya isa wurin inda ya ke fada wa manema labarai cewa: "Ba za a karya mana gwiwa ba."
Wannan na zuwa ne bayan harin da wani dan cirani dan asalin kasar Tunisia ya kai a wata coci da ke Nice inda ya halaka mutum uku.
KU KARANTA: An kama ɗan tsohon ministan Najeriya ya tafi yin fashi da makami a Abuja
Har wa yau, kwanaki kaɗan baya sai da wani mahari ya datse kan wani malamin makaranta a ƙasar bayan malamin ya nuna wa ɗalibansa wasu hotunan zanen ɓatanci da aka yi ga manzon Allah, Annabi Muhammad SAW.
A wani labarin, An cigaba da zanga-zanga, ranar Juma'a, a wasu ƙasashen Musulmi don nuna fushi kan kalaman shugaban Faransa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
An cigaba da zanga-zanga bayan sallar Juma'a a wurare daban-daban a zirin Gaza inda kungiyar Hamas ta bukaci masu zanga-zangar su hadu a sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia don cigaba da nuna fushin su kan batun.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng