Uwargidan gwamnan Kebbi ta yi martani mai zafi ga matashin da ya zargesu da nada 'yan uwa kwamishinoni

Uwargidan gwamnan Kebbi ta yi martani mai zafi ga matashin da ya zargesu da nada 'yan uwa kwamishinoni

- Matar mai girma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudo ta mayar da martani ga wani a Twitter, bayan yayi mata tsokacin da taga bazata iya kyalesa ba

- Ta wallafa hotunan wasu kwamishinonin jihar Kebbi masu kananun shekaru a ranar matasa ta kasa, inda tace yakamata a dinga ba matasa dama

- Sai saurayin yace ai daga gani 'yan uwan gwamnan ne, shine tace eh! 'Yan uwanta ne, Idan ya samu irin wannan damar ya dora makiyansa

Najeriya tayi shagalin zagayowar ranar matasa ta kasa a ranar 1 ga watan Nuwamba.

Don nuna farinciki, matar gwamnan jihar Kebbi, Zainab Bagudu ta wallafa hotuna 5 na kwamishinonin jihar masu karancin shekaru, inda take nuna basu wuce shekaru 30 zuwa 40 ba don bunkasa kasa.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter: "A jihar Kebbi, Gwamna Atiku Bagudu ya zabi kwamishinoni da ke tsakanin shekaru 30 zuwa 40. Najeriya za ta samu cigaba ne idan aka bai wa matasa dama. Barka da ranar matasa ta kasa."

Bayan wannan wallafar ne wani yayi tsokaci a kai, inda ya ce ya san kwamishinonin da mijinta ya zaba 'yan uwa ne da abokan arzikinsa.

Bayan ganin wannan tsokacin ne ta mayar masa da martani, inda ta rubuta: "Eh. Iyayena da iyayensu uwa daya uba daya suke. Idan ka samu dama irin wannan, ka zabo makiyanka ka dora."

Uwargidan gwamnan Kebbi ta yi martani mai zafi ga matashin da ya zargesu da nada 'yan uwa kwamishinoni
Uwargidan gwamnan Kebbi ta yi martani mai zafi ga matashin da ya zargesu da nada 'yan uwa kwamishinoni. Hoto daga @DrZSB
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Kada ku ji tsoro, ku fito mu tattauna - Buhari ga matasa

KU KARANTA: 'Yan adawa ke daukar nauyin 'yan daba domin lalata mulkina - Gwamnan PDP ya koka

A wani labari na daban, bayan taron da jami'an tsaro suka yi a wuraren da zanga-zangar EndSARS ta fi shafa a kudancin Najeriya, wani dan sanda wanda baiso a bayyana sunansa ba, cikin wadanda sukaje taron yace bai dace ace 'yan Najeriya sun tayar da tarzoma ba.

Dan sandan, wanda DPO ne, ya sanar da PRNigeria a wata hira, cewa kamata yayi a ce 'yan Najeriya na iyakar kokarinsu wurin kiyaye kansu daga 'yan ta'adda da bata-gari a wannan lokacin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel