Da duminsa: Sabbin mutum 170 sun harbu da korona a Najeriya

Da duminsa: Sabbin mutum 170 sun harbu da korona a Najeriya

- Hukumar NCDC ta bayyana cewa sabbin mutum 170 sun sake harbuwa da cutar korona

- Sun sanar da faruwar hakan a ranar Juma'a 30 ga watan Oktoban 2020

- Kamar yadda suka bayyana, jihar Legas ce ke da kaso mafi yawa inda ta samu mutum 106

Alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC), na ranar Juma'a 30 ga watan Oktoban 2020 sun bayyan cewa sabbin mutum 170 sun harbu da cutar korona a Najeriya.

Lagos-106

FCT-25

Oyo-14

Edo-7

Kaduna-7

Ogun-4

Bauchi-2

Benue-2

Kano-1

Osun-1

Rivers-1

KU KARANTA: FRSC ta umarci jami'anta da su koma kan tituna

Jimillar wadanda suka kamu da cutar a Najeriya sun kai 62691, mutum 58,430 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar.

Mutum 1044 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar.

KU KARANTA: Saurayi ya biya wa budurwa 432,000 a mashaya, ta ki sauraronsa kuma ta bi wani saurayi

A wani labari na daban, Salamatu Abubakari wata mata ce 'yar Ghana mai yara 3, ta bayyana yadda tayi shekaru 20 tana aikin fentin mota.

Yanayin matar ya nuna bata wuce shekaru 35 ba a wata hira da Legit.ng suka yi da ita wacce gidan talabijin din SV suka nuna.

A cewarta, sana'ar ta kasance wacce maza suke yi, don haka ta fuskanci kalubale iri-iri, amma saboda dagewarta kwarewa a harkar, sai ta saba.

Kamar yadda tace: "Da farko na tsani sana'ar saboda ni kadai ce macen da ta ke sana'ar kuma ina shan wahala.

"Amma bayan shekaru 20, ga yara 3, sana'ar ta bi jikina, har ina taimakon iyalina da ita."

A karshe, ta bayyana abinda yafi damunta, shine yadda samari da dama suke kawo mata tayin soyayyarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel