Iyaye da 'yan uwa sun mayar da 'yan gidan fursuna 24 zuwa gidan kaso a Benin

Iyaye da 'yan uwa sun mayar da 'yan gidan fursuna 24 zuwa gidan kaso a Benin

- Lauyoyi, iyaye da 'yan uwan fursunonin da suka tsere daga gidajen gyaran hali da ke jihar Edo sun mayar da su

- Hakan ya biyo bayan umarnin gwamnan jihar, inda yace duk wani fursuna da ya gudu yayi gaggawar komawa gidan

- Duk da dai wata majiya daga gidan gyaran halin ta ce wadanda suka koma gidan ba masu manyan laifuka bane

Dangin fursunoni 1,181 daga cin wadanda suka gudu daga gidajen gyaran hali na Oko da Benin sun maido dasu da kansu, jaridar Leadership ta wallafa hakan.

Wata majiya daga gidan gyaran halin ta tabbatar da cewa 'yan uwan mutane 24 daga cikin wadanda suka gudu sun dawo dasu tare da lauyoyinsu a ranar 30 ga watan Oktoba, 2020, a bisa umarnin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Dama gwamnan ya umarcesu da su yi gaggawar komawa ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

KU KARANTA: Salamatu Abubakar: Mahaifiyar yara 3 da ke fentin mota a matsayin sana'a

Idan baku manta ba, bata-gari sun yi amfani da damar zanga-zangar EndSARS wurin kai wa gidajen gyaran hali da ke jihar Benin farmaki, inda suka saki fursunonin.

Wata majiya ta bayyana yadda iyaye da 'yan uwan 24 daga cikin wadanda suka tsere suka maido dasu da taimakon lauyoyinsu.

Iyaye da 'yan uwa sun mayar da 'yan gidan fursuna 24 zuwa gidan kaso a Benin
Iyaye da 'yan uwa sun mayar da 'yan gidan fursuna 24 zuwa gidan kaso a Benin. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Dakarun soji sun kashe 'yan ta'adda, sun bankado harin tawagar 'yan gudun hijira

"Muna jiran sauran su cigaba da dawowa. Duk da yawancin wadanda suka dawo sun kusa karasa kwanakin da ya kamata su yi a gidajen gyaran halin, masu munanan laifuka daga cikin su kuma basu riga sun dawo ba," a cewarsa.

A wani labari na daban, rundunar sojoji sun kashe fiye da 'yan ta'adda 3, yayin da suke kokarin kai wa tawagar masu mayar da 'yan gudun hijira zuwa garin Baga daga Maiduguri.

Kamar yadda kakakin rundunar, manjo janar John Enenche ya shaida, an kwaci miyagun makamai a hannunsu, bayan sun kama wani mai garkuwa da mutane a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba.

Enenche, ya bayyana hakan a hedkwatar tsaro da ke Abuja, yayin gabatar da jawabin sati a kan harkar tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel