Da duminsa: EFCC ta yi wa tsohon shugaban FIRS kiran gaggawa

Da duminsa: EFCC ta yi wa tsohon shugaban FIRS kiran gaggawa

- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gayyaci tsohon shugaban hukumar kudin shiga ta kasa

- Kamar yadda aka tabbatar daga EFCC, Fowler ya amsa kiran inda ya je ofishin hukumar a Legas

- Kakakin hukumar EFCC ya tabbatar da hakan amma bai san dalilin wannan gayyatar ba

Tsohon shugaban hukumar kudin shiga (FIRS), Babatunde Fowler ya bayyana gaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da hakan ga jaridar Premium Times a ranar Litinin.

Ya ce, "An gayyacesa zuwa hukumar kuma ya amsa kiran inda ya ziyarci ofishinmu da ke Legas."

Uwujaren bai sanar da dalilin da yasa aka gayyaci Fowler zuwa ofishinsu ba.

Fowler, wanda ya kasance shugaban hukumar FIRS na farko ya kwashe shekaru takwas yana mulki kuma an sallamesa a watan Disamban shekarar da ta gabata.

KU KARANTA: EndSARS: Kwamitin bincike na jihar Legas sun ziyarci ma'adanar gawawwaki ta soji

Da duminsa: EFCC ta yi tsohon shugaban FIRS kiran gaggawa
Da duminsa: EFCC ta yi tsohon shugaban FIRS kiran gaggawa. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Sabbin mutum 170 sun harbu da korona a Najeriya

A wani labari na daban, Aawata takarda ta ranar Juma'a, Bisi Kazeem, Kakakin hukumar FRSC yace shugaban hukumar, Boboye Oyeyemi, ya bayar da umarni, inda yace jami'an FRSC su cigaba ta kula da tituna yadda ya dace.

Ya bayar da wannan umarnin ne bayan mutane 21 sun rasa rayukansu bayan wata babbar mota ta murkushe wata motar 'yan makaranta a jihar Enugu, The Cable ta ruwaito.

"Wadanda mummunan hatsarin jihar Enugu ya ritsa dasu, cikin mutane 56, 21 sun rasa rayukansu," a cewarsa.

Hatsarin ya faru ne a kan kwanar Nkwo/Mmaku, kusa da tsohon titin Enugu/Okigwe a daidai karfe 4 na yamma a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, 2020, tsakanin wata mota kirar Marsandi (ENU 811KU) dauke da yara 'yan makaranta da wata babbar mota Flatbed Mack Truck (KPP 247 XA).

A cewarsa, "Hatsarin ya faru ne saboda matsalar birkin mota. Duk da hare-haren da bata-gari suka kai wa ofisoshin FRSC, inda suka lalata wasu abubuwa, suka saci wasu suka kuma kona wasu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng