Babu dan Najeriyan da zai ce ba'a samu canji ba - Ministan Lantarki

Babu dan Najeriyan da zai ce ba'a samu canji ba - Ministan Lantarki

- A hira ta musamman, Saleh Mamman ya yi bayanin halin da lamarin wutan lantarki ke ciki

- Ya ce gwamnati ta tsame hannunta daga cikin harkar wuta gaba daya

- Ya jaddada cewa babu yadda gwamnati ta iya kan lamarin karin farashin wuta

Ministan wutan lantarki, Injiniya Saleh Mamman ya bayyana cewa babu dan Najeriyan da zai ce ba'a samu canji a bangaren wuta ba karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

Buhari ya nada Saleh Mamman ministan lantarki baya nasara a zaben 2019.

Ya gaji Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje na yanzu.

A hirar da yayi da BBC Hausa, Saleh Mamman ya ce kashi 80 zuwa 90 na masu samun wutan lantarki zasu tabbatar an samu canji na wutan lantarki.

Ya ce gaba daya Najeriya an samu karin wutan lantarki karkashin gwamnatin Buhari.

Ya kara da cewa babu gari ko anguwar da zata ce ta kwana daya ba'a kawo wuta ba sai da idan wani abu ya lalace.

Yace: "Kashi 90 ko 80 daga cikin yan Najeriya dake samun wutan lantarki, tsakani da Allah idan ka tambayesu ko akwai canji, wallahi zai fada maka akwai canji."

"Babu gari ko wani gefe a kasar nan wanda zai ce maka an wuni tun daga safe har dare ba'a kawo mashi wuta ba, da sharadi guda, sai dai akwai matsala. Wakil taransfoman unguwarsu ta samu matsala ko ta lalace."

"Amma ina tabbatar maka cewa tun da muka kama ragamar mulki, babu garin da za'a waye gari tun daga safe har dare ba'a samu wuta."

KU KARANTA: Kuma dai: Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun halaka mutum 4

Babu dan Najeriyan da zai ce ba'a samu canji ba - Ministan Lantarki
Babu dan Najeriyan da zai ce ba'a samu canji ba - Ministan Lantarki
Asali: Facebook

A bangare guda, mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa ba talauci ta tunzura mutane wawushe runbunan abinci da shaguna ba a fadin tarayya, kwadayi ce kawai.

Adesina wanda ya bayyana hakan a hirar da yayi a shirin Sunrise Daily na tashar Channels TV ya ce malalata da batagari ne kawai sukayi amfani da zanga-zanga wajen satan kayan abinci.

Ya ce sam bai amince da bayanan da wasu ke yi ba cewa yunwa ta sa mutane ke wawusan kayan abinci ba.

KU KARANTA: Kuma dai, yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara, sun yi kashe rai

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel