Najeriya zata yi duk yadda zata yi don ganin ta kaucewa annobar COVID-19 a karo na biyu p- Buhari
- Rahotanni daga nahiyar Turai na nuni da cewa annobar korona kan iya dawowa da karfinta a karo na biyu
- Kasashen duniya sun saka dokar ta baci sakamakon ballewar annobar korona a karo na farko, lamarin da ya jefa jama'a da yawa cikin kunci
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa tattalin arziki bashi da karfin da zai juri a sake rufe shi a karo na biyu
A wani jawabi da shugaban kasa, Muhammad Buhari, ya wallafa a shafinsa na tiwita a ranar Alhamis ya ce tattaƙin arziƙin Najeriya bashi da ƙwarin da zai iya jure wani sabon kullen.
"Duba da irin halin da wasu ƙasashe ke ciki, ya zama dole muyi duk yadda za muyi don kaucewa ɓullar annobar COVID-19 a karo na biyu.
"Ya zama wajibi a kanmu mu tabbatar ba mu sake komawa gidan jiya ba.
DUBA WANNAN: An samu bindigu 65 a wurin masu laifi 157 da aka kama a Kaduna
"Tattalin arziƙin mu bai da ƙwarin da zai iya jure sake shiga halin da muka shiga na kulle,ba shiga ba fita," kamar yadda shugaba Buhari ya rubuta.
A watan Maris ne shugaba Buhari ya saka dokar kulle a wasu Jihohi da suka haɗa da Legas, Ogun, da kuma birnin tarayya, Abuja, domin daƙile yaɗuwar annobar cutar Korona.
DUBA WANNAN: An sace $2m daga kudin yakin neman zaben Trump a Amurka
A sakamakon hakan, an samu koma baya a al-amurran tattalin arziƙi, ribar cikin gida da ƙasa ke samu (GDP) ta ragu da kaso 6.1% a watanni huɗun farkon shekarar 2020.
Asusun ajiya na ƙasar waje shi ma ya ragu da kaso 4.3% a shekarar 2020, wanda hakan ya jawo matsin tattalin arziƙi a karo na biyu cikin shekara biyar.
Adadin masu cutar COVID-19 na ɗaɗa raguwa inda tuni lamurra suka fara dai-daita a Najeriya.
A cigaba da kama daidaikun mutane da cutar ke yi, Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa shahararren dan wasan kasar Juventus Cristiano Ronaldo ya samu waraka daga muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus, kungiyar ta tabbatar ranar Juma'a.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng