ENDSARS:Ƴan gwagwarmaya sun sauya salo,sun sake miƙawa gwamnati sababbin buƙatu 7
- Har yanzu wasu daga cikin kungiyoyin da suka assasa tare da jagorantar zanga-zangar ENDSARS basu hakura da gwagwarmaya ba
- Rahotanni sun bayyana yadda wasu kungiyoyi suka fara barazanar sake fitowa domin cigaba da zanga-zangar da tashin tarzoma ya katsewa hanzari
- A wannan karon, wasu kungiyoyin 'yan gwagwarmaya sun mikawa gwamnati sabbin bukatu guda 7 da suke so a gaggauta zartar dasu
A ƙoƙarin farfaɗowa daga guguwar zanga-zangar kawo ƙarshen SARS(#EndSARS), haɗakar ƙungiyoyi gwagwarmaya kare haƙƙin ɗan adam sun sauya salon inda aka nufa.
Ƙungiyoyin sun miƙawa gwamnati sababbin ƙudiri har guda bakwai(7) wanda suke da muradin ganin gwamnati ta biya buƙatun cikin kudirrirrikan nasu.
Haɗakar ta zo ne bayan taron tattaunawa na tsawon kwana guda da ƙungiyoyin suka gudanar ƙarƙashin inuwar NNN (New Nigeria Network) wacce ke nufin 'tsarin sabuwar Najeriya'.
Daga cikin ƙungiyoyin da ke cikin haɗakar akwai: Radical Agenda Movement in the Nigeria Bar Association (RAMINBA), kungiyar ma'aikatan yau da kullum, Ƙungiyar masu neman juyin juya hali a Najeriya (CORE), da sauran su.
KARANTA: Tirkashi: An samu bindigu 65 a wurin masu laifi 157 da aka kama a Kaduna
Ƙungiyoyin sun ce suna nan sun kusa kawo ƙarshen bincike akan wulaƙanci da zaluncin da aka yiwa masu zanga-zangar lumana ba tare da makami ba.
Ƙungiyar sabon tsarin Najeriya (NNN) haɗakar ƙungiyoyi ne da suka bada cikakkiyar gudunmawa yayin gudanar da zanga-zangar kawo ƙarshen SARS (#EndSARS).
Acewar shugaban RAMINDA, Barista Adesina Ogunlana, sabbin ɓukatun sun haɗar da;
KARANTA: An sace $2m daga kudin yakin neman zaben Trump a Amurka
1. A hazanzarta biyan buƙatunsu na farko da aka alƙawarta musu,
2. A gaggauta canja Shugaban rundunar ƴansanda.
3. A hanzarta dawo da kuɗin wuta da man fetur yadda suke a baya.
4. A gaggauta tsayar da biyan albashi mai tsoka ga ƴan siyasa da masu riƙe da maƙaman siyasa.
5. A sanya dukkan ma'aikatun gwamnati a sabon tsarin biyan mafi ƙarancin albashi.
6. A ƙara yawan kuɗin da ake warewa ɓangaren ilmi da kuma lafiya.
7. Gwamnati ta gaggauta maida ɓangaren wuta da man fetur zuwa hannunta.
A ranar Juma'a ne Legit.ng Hausa ta wallafa labarin cewa 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, ta yi shagube ga Musulman da suka dinga caccakarta saboda 'ta yi uwa, ta yi makarbiya' a zanga-zangar ENDSARS.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng