Yanzu-yanzu: Shahrarren da kwallon duniya, Cristiano Ronaldo, ya warke daga cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: Shahrarren da kwallon duniya, Cristiano Ronaldo, ya warke daga cutar Coronavirus

- Bayan kwanaki 19 a killace, Cristiano Ronaldo ya samu waraka

- Babban dan kwallon ya rasa muhimmiyar wasar tsakanin Juventus da Barcelona

- Juventus ta sha kashi a gida a wasar ga gasar zakarun Turai

Shahrarren dan wasan kasar Juventus Cristiano Ronaldo ta samu waraka daga muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus, kungiyar ta tabbatar ranar Juma'a.

"Ronaldo ya yi gwajin cutar. Sakamakon ya nuna cewa ya samu waraka," Juventus tace.

"Saboda haka, dan kwallo ya warke bayan kwanaki 19 kuma babu bukatar killace kansa yanzu."

Ronaldo ya kamu da cutar COVID-19 ne ranar 13 ga watan Oktoba yayin wasar kasarsa, Portugal. Ya killace kansa tun lokacin da ya kowa Italiya.

Shahrarren dan kwallon ya yi rashin wasanni hudu, harda wasa da tsohon abokin hamayyarsa Lionel Messi, a gasar zakarun Turai, inda kungiyarsa ta fadi ci 2-0.

Kungiyar kwallon Juventus wacce ta lashe kafin Seria A a kakar da ta shude na matsayi na biyar yanzu haka a tebur.

Yanzu-yanzu: Shahrarren da kwallon duniya, Cristiano Ronaldo, ya warke daga cutar Coronavirus
Yanzu-yanzu: Shahrarren da kwallon duniya, Cristiano Ronaldo, ya warke daga cutar Coronavirus
Asali: Getty Images

A wani labarin daban, an saki ranakun buga wasar fiddan gwanin gasar kasashen nahiyar Afrika tsakanin Najeriya da kasar Sierra Leone.

Wanna itace wasa ta farko da yan kwallon Najeriya zasu buga domin samun gurbin shiga sahun kasashen da zasu kara a gasar Afcon 2022.

Za'a buga wasanni biyu tsakanin dukkan kasashe; daya a gida, daya a waje.

A wasar farko, Najeriya zata karbi bakuncin yan kwallon kasar Sierra Leone a filin kwallon Samuel Ogbemudia dake birnin Benin, jihar Edo ranar Juma'a, 13 ga watan Nuwamba, 2020.

Bayan haka yan kwallon Najeriya zasu garzaya filin kwallon Siaka Stevens dake Freetown, kasar Sierra Leone ranar 17 ga Nuwamba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel