Mun sa kafar yaki da akidun addinin Islama, in ji kasar Faransa

Mun sa kafar yaki da akidun addinin Islama, in ji kasar Faransa

- Kasar faransa ta bayyana cewa za ta daura damarar yaki da akidun addinin Islama

- Hakan ya biyo bayan halaka wasu mutane uku da aka yi a wata coci da ke yankin kudancin birnin Nice

- Yan sanda dai sun harbi wanda ake zargi da harbin Nice inda yake kwance cikin mawuyacin hali a asibiti

Rahotanni sun kawo cewa kasar Faransa ta sha alwashin daura damarar yaki da akidun addinin Islama.

Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Gerald Darmanin, ne ya bayyana hakan bayan kisan wasu mutane uku a wata coci da ke kudancin Nice, Sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

Darmanin ya yi gargadin kara samun irin wadannan hare-hare, amma kuma ya jaddada cewa kasar Faransa ba ta yaki da wani addini.

Shugabar masu adawa a kasar, Marine Le Pen ta yi kira ga gwamnati a kan ta samar da dokokin gaggawa domin tasa keyar masu kaifin kishin Islama zuwa kasashensu na asali.

KU KARANTA KUMA: An kashe 'yan sanda 22 da lalata ofisoshinsu 205 a zanga-zangar EndSARS

Mun sa kafar yaki da akidun addinin Islama, in ji kasar Faransa
Mun sa kafar yaki da akidun addinin Islama, in ji kasar Faransa Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron zai sake kiran wani taro na majalisar tsaro domin tattauna batun harin na Nice da kullen COVID-19, wanda ya fara aiki da tsakar dare.

A yanzu haka, wanda ake zargi da kisan na birnin Nice na cikin mawuyacin hali a asibiti bayan jami’an 'yan sanda sun harbe shi.

KU KARANTA KUMA: Bukin Maulud: Muhimman abubuwa 5 da Buhari ya faɗa wa yan Nigeria

A wani labari na daban, Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya taya al’umman Musulmi a jiharsa murnar zagaowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

Obaseki ya ja hankalin Musulman jihar a kan su ci gaba da koyi da kyawawan halayen manzon tsira.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a cikin jawabin maulidin Annabi da ya ke gudana a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel