An kashe 'yan sanda 22 da lalata ofisoshinsu 205 a zanga-zangar EndSARS

An kashe 'yan sanda 22 da lalata ofisoshinsu 205 a zanga-zangar EndSARS

- Rundunar yan sanda ta musanta zargin da kungiyar Amnesty International ta yi na cewa jami'anta sun harbi masu zanga-zangar lumana

- Sufeto janar na yan sanda ya ce an kashe masu jami'ai 22 tare da kona masu ofishoshi 205 duk a zanga-zangar

- Ya ce sabanin rahoton kungiyar kare hakkin dan adam din, jami'ansu basu yi harbi ba illa kare masu zanga-zangar da suka yi

Akalla jami’an yan sanda 22 aka kashe sannan aka raunata wasu da dama a yayin zanga-zangar EndSARS, hedkwatar rundunar yan sandan Najeriya, Abuja ta bayyana.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DCP Frank Mba, a ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa wasu da dama na cikin matsanancin sakamakon raunukan da suka samu yayinda aka kona ofishin an sanda 205 a yayin zanga-zangar, The Nation ta ruwaito.

Mba, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa bata garin da suka janye zanga-zangar sun kuma lalata wasu ,muhimman gine-gine masu zaman kansu da na gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Ka ji matsalarmu da sabon tsarin biyan albashin Malamai inji Gwamnonin Najeriya

An kashe 'yan sanda 22 da lalata ofisoshinsu 205 a zanga-zangar EndSARS
An kashe 'yan sanda 22 da lalata ofisoshinsu 205 a zanga-zangar EndSARS Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Rundunar yan sandan ta ce duk da irin wannan barnar da aka yi musu yayin wannan zanga-zangar, ba ta fito ta yi amfani da karfin iko ba ko kuma harbin masu zanga-zangar.

Hukumar yan sandan ta kuma yi watsi da rahoton kungiyar Amnesty International, wacce ta cewa 'yan sandan kasar sun harbi masu zanga-zangar lumana.

KU KARANTA KUMA: An kashe 'yan sintiri hudu da wasu yayin da 'yan bindiga suka kai hari a Katsina

Ta jaddada cewa jami’anta sun yi aiki cike da kwarewa, sun nuna bajinta wurin tabbatar da cewa an yi zanga-zangar lumana, a wani lokaci ma sukan tsaya a gefen masu zanga-zangar domin kare su.

Jawabin ya zo kamar haka: “Babban Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya, Mohammad Adamu, ya tabbatar da cewa 'yan sandan kasar sun yi aiki bisa kwarewa, sun nuna bajinta sannan wasu sun sadaukar da ransu don zaman lafiya a yayin zanga-zangar kwanaki da rikicin da ya barke a wasu yankunan kasar.

“IGP ya yi wannan tsokaci ne sakamakon rahoton Amnesty International na ranar 21 ga watan Oktoba, 2020 cewa jami’an yan sanda sun harbi masu zanga-zangar lumana. Ya bayyana rahoton kungiyar a matsayin karya, mai batarwa kuma wanda ya sha bamban da duk wata hujja da ake da ita a kasa.

“IGP ya bayyana cewa a yayin zanga-zangar, jami’an rundunar sun yi amfani da hanyar da ta dace wajen tabbatar da ganin cewa an yi zanga-zangar cikin lumana, a wani lokaci ma sukan tsaya a gefen masu zanga-zangar domin kare su.

“Rahotannin da aka samu sun nuna cewa masu zanga-zangar sun kashe 'yan sanda 22 da raunata da dama daga cikinsu, kuma akasarin 'yan sandan da aka raunata na cikin matsanancin hali.

“Masu zanga-zangar sun kuma lalata ofishin yan sanda 205 sannan suka lalata gine-gine masu zaman kansu da na gwamnati.

“Duk da cewa an samu rikici a lokacin zanga-zangar a wasu sassa na ƙasar, 'yan sandan ba su yi amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima ba wurin kwantar da tarzomar.

“Ta kuma yi Alla-wadai da halin Amnesty International na kin ambata ko karrama jami’an yan sandan da aka kashe a lokacin zanga-zangar yayinda suke bauta wa kasarsu.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa an samu ‘Yan iskan gari da su ka shiga cikin inuwar zanga-zangar #EndSARS sun kashe wani ‘dan sanda a jihar Ebonyi.

Wadannan tsagerun mutane sun kai hari a ofishin ‘yan sanda a garin Abakiliki, inda su ka karbe bindigar wannan jami’in tsaro, Inspector Egu Omini.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel