Ka ji matsalarmu da sabon tsarin biyan albashin Malamai inji Gwamnonin Najeriya

Ka ji matsalarmu da sabon tsarin biyan albashin Malamai inji Gwamnonin Najeriya

- Kwanakin baya shugaban kasa ya bada sanarwar ya kara wa malamai albashi

- Gwamnoni sun nuna ba su da kudin da za su kara albashin Malaman jihohinsu

- Gwamnatin tarayya ta dauki wannan mataki ba tare da ta tuntubi gwamnoni ba

The Nation ta ce muddin ba a cika sharuda ba, malaman makarantun gwamnatin tarayya kadai za su amfana da sabon tsarin albashin da aka shigo da shi.

Gwamnonin jihohin kasar nan sun yi mamaki da su ka ji shugaba Muhammadu Buhari ya bada sanarwar karin albashin malamai ba tare da tuntubar su ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnoni su na banbami a kan wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka ita kadai, duk da jihohi su na da ta cewa.

KU KARANTA: Ba Malamin Jami’a ba ne sai fadi yadda za a biya shi albashi – Gwamnati

Alamu sun nuna kungiyar gwamnoni na NGF za ta nemi ta gana da ministan ilmi, Malam Adamu Adamu, domin a shawo kan matsalolin da za a iya fuskanta.

Wata matsala da za a iya samu yanzu ita ce, gwamnatin tarayya ba ta yi la’akari da cewa akwai jihohin da tuni su ke biyan malamansu albashi na musamman.

Wasu gwamnoni sun fara kiran a yi wa dokar UBE garambawul, ta haka gwamnoni za su samu karin kudi da za su iya biyan malamai sabon tsarin albashin.

“Ministan ya tabbatar wa gwamnoni cewa shugaba Muhammadu Buhari ya na da manufa mai kyau.” Majiyar ta ce NGF za ta zauna da gwamnatin tarayya.

KU KATANTA: Babu abin da ya canza zani, ASUU ta soki gwamnatin Shugaba Buhari

Matsalarmu da sabon tsarin biyan albashin Malamai inji Gwamnonin Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Wani gwamna da ya yi magana ba tare da ya bari an kama sunansa ba, ya nuna za su a jinkirta wannan kari ta yadda za su sa kudin a cikin kundin kasafinsu.

Kafin sauya-sauyen da shugaban kasa ya yi alkawari su fara aiki, dole ma sai an yi wa dokokin TETFUND kwaskwarima, kafin a iya kara masu wasu dawainiya.

Gwamna Nyesom Wike shi ne wanda ya fara fito wa ya soki matakin da gwamnatin tarayya ta dauka, ya ce sabon tsarin albashin malaman zai jawo matsala.

Nyesom Wike ya soki yadda gwamnatin tarayya ta kara albashin malamai ba tare da ta tuntubi jihohi domin a ji yadda za a sake tsarin rabon kason arziki ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng