‘Yan iskan gari sun yi wa ‘Dan Sanda lahani, sun kashe shi a Jihar Ebonyi

‘Yan iskan gari sun yi wa ‘Dan Sanda lahani, sun kashe shi a Jihar Ebonyi

- ‘Yan Sanda sun tabbatar da mutuwar wani Jami’insu a Abakaliki, jihar Ebonyi

- An kai hari a ofishin ‘Yan Sanda, an yi barna ta kin karawa a cikin makon nan

- Tsagerun sun kashe ‘Dan Sanda, sun datse masa al’aura, sun bankawa ofis wuta

Jaridar Vanguard ta ce an samu ‘Yan iskan gari da su ka shiga cikin inuwar zanga-zangar #EndSARS sun kashe wani ‘dan sanda a jihar Ebonyi.

Wadannan tsagerun mutane sun kai hari a ofishin ‘yan sanda a garin Abakiliki, inda su ka karbe bindigar wannan jami’in tsaro, Inspector Egu Omini.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ebonyi, Philip Maku ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, ya ce sai da aka cire zakarin jami’in tsaron kafin a kashe shi.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda a Najeriya

CP Philip Maku ya bayyana haka ne ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda ta Ebonyi, Loveth Odah, a wani jawabi da ta aika wa manema labarai jiya.

Loveth Odah ta ce ‘yan iskan gari sun auka wa babban ofishin ‘yan sanda na Abakaliki a ranar Litinin 26 ga watan Oktoba, wannan shi ne karo na biyu.

“Tsagerun sun kona motocin aikin ‘yan sanda da babura da sauran kaya da jami’an tsaro su ka karbe. Daga nan su ka shiga harbi ko ta ina.” Inji Odah.

KU KARANTA: EndSARS: Ministoci su kawo mani rahoton abin da su ka gani – Buhari

‘Yan iskan gari sun yi wa ‘Dan Sanda lahani, sun kashe shi a Jihar Ebonyi
Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Ebonyi Hoto: www.pmnewsnigeria.com/2020/06/09/maku-assumes-office-as-ebonyi-commissioner-of-police
Asali: UGC

Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan ta ce: “A dalilin haka su ka yi wa Insp. Egu Omini kisan-gilla, su ka datse zakarinsa, su ka dauke bindigarsa.”

A wannan hari da aka kai, an yi ta’adi iri-iri, har kuma an harbi wani ‘dan sanda mai suna Insp. Okewu Sunday, an kuma karbe masa bindigarsa ta AK-47.

A ranar farko da aka kai wannan hari, an raunata wasu ‘yan sanda; Paul Akpu da PC Ali Samson, a dalilin haka, Akpu ya rasu a wani asibitin gwamnati.

A jiya kun ji cewa gwamnati ta shiga kotu da mutane 300 da aka kama sun wawuri kayan tallafi.

Tsagerun da su ka saci dukiyar Jama’a a lokacin zanga-zangar #EndSARS a yankunan Jos da Bukuru a Filato za su tafi kukurku ko kuma su biya tara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng