Zamfara: An yi batakashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga, ba a san adadin wadanda suka mutu ba

Zamfara: An yi batakashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga, ba a san adadin wadanda suka mutu ba

- Har yanzu ba a daina samun rahotannin cewa 'yan bindiga sun kai hari ba a jihar Zamfara

- A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa sun shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma

- Rundunar soji da ta 'yan sanda sun kaddamar da atisaye daban-daban domin kawo karshen 'yan bindiga a jihohin Katsina, Sokoto, da Zamfara

A ranar Alhamis ne wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan bindiga ne suka yi musayar wuta da dakarun rundunar soji a kauyen Gidan Goga da ke yankin karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Daily Trust ta rawaito cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari Gidan Goga a kan babura da misalin karfe 1:00 na ranar Alhamis.

Mazauna kauyen sun sanar da Daliy Trust cewa 'yan bindigar sun budewa jama'a wuta bayan shigarsu kauyen kafin daga bisani su yi awon gaba da shanu da sauran dabbobin da ake kiwo a gida.

Zamafara: An yi batakashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga, ba a san adadin wadanda suka mutu ba
Zamafara: An yi batakashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga, ba a san adadin wadanda suka mutu ba @Daily_Trust
Asali: Twitter

Wani tsohon kwamishinan ilimi a jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga, ya tabbatarwa da Daily Trust cewa 'yan bindiga sun kai hari kauyen da misalin karfe daya na rana.

"An sanar da sojoji kuma sun yi sa'ar zuwa sun tarar da 'yan bindigar kafin su gudu.

DUBA WANNAN: Sabon hari a Katsina: Yan bindiga sun sace mata uku yayin artabu da 'yan sanda

"An yi musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindigar, ba zan iya cewa ga adadin mutanen da suka mutu ba, amma na san cewa mutane da yawa sun bar gidajensu," a cewarsa.

Kafin wallafa wannan rahoto, Daily Trust ba ta samu kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, a waya ba domin jin ta bakinsa a kan kai harin.

A ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa ta shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng