Mun gode da baku zama ɓarayi irin sauran ba: Buhari ya jinjina wa matasan Borno

Mun gode da baku zama ɓarayi irin sauran ba: Buhari ya jinjina wa matasan Borno

- Matasan Borno sun sha jinjina daga wajen shugaba Buhari kan yadda suka kama kansu yayinda sauran mutane ke ta sace-sace da lalata kayayyaki a sauran jihohi

- Gwamnan jihar, Babagana Zulum, shima ya yi alfahari da matasan wadanda suka kwantar da hankalinsu a yayin zanga-zagar EndSARS a kasar

- Ku tuna cewa zanga-zangar EndSARS wacce ta fara cikin lumana ta koma rikici bayan wasu bata gari sun janye ragamar ta, sun yi ta lalata kayan gwamnati da na mutane

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba ma matasan Borno, kan kin shiga sahun masu barnar kaya da sace-sace sakamakon zanga-zangar EndSARS da aka yi a kasar.

Karamin ministan noma, Alhaji Buba Shehuri ne ya bayyana hakan, inda ya ce Buhari ya jinjinawa matasan a wani sakon fatan alkhairi zuwa ga kungiyar masu ruwa da tsaki na zaman lafiya a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, a Maiduguri.

A cewarsa, Buhari na matukar alfahari da matasan Borno wadanda suka nuna halin dattako da nagarta ta hanyar kin shiga rikicin karkashin fakewa da zanga-zangar EndSARS, PM News ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Bukin Maulud: Muhimman abubuwa 5 da Buhari ya faɗa wa yan Nigeria

Mun gode da baku zama ɓarayi irin sauran ba: Buhari ya jinjina wa matasan Borno
Mun gode da baku zama ɓarayi irin sauran ba: Buhari ya jinjina wa matasan Borno Hoto: @ProfZulum
Asali: Twitter

Ya ce Shugaban kasar ya kuma jinjinawa gwamnan Borno, Babagana Zulum, da sauran masu ruwa da tsaki kan rawar ganin da suka taka wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Buba-Shehuri ya nuna irin alfaharin da yake yi da Zulum wanda ya tabbatar da ganin cewa an raba kayan tallafin korona da sauran kayan agaji ga mutane a jihar.

Ya ce: “Shugaban kasar ya yi farin ciki da jajircewar gwamnan da gudunmawarsa wajen yaki da ta’addanci, aikin taimakawa jama’a, mayar da yan gudun hijira muhallinsu da sauran tsare-tsare.”

KU KARANTA KUMA: 2023: Kudu maso gabas ne ya kamata ya samar da magajin Buhari – Gwamna Umahi

Da yake nasa jawabin, Shehun Borno, Abubakar Umar-Garbai Ibn El-Kanemi, ya yi godiya ga matasan a kan kwantar da hankalinsu da sukayi da kuma kin shiga zanga-zangar.

A nashi martanin, Zulum ya jaddada jajircewarsa ga shugabanci nagari da kuma jinjinawa matasan a kan kame kansu da suka yi a wannan lokaci da ake ciki.

A gefe guda, mun ji cewa mazauna Lagas sun roki jami’an yan sanda da su koma bakin aiki sannan su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, jaridar The Nation ta ruwaito.

Sun yi wannan roko ne a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, a kafofin soshiyal midiya sakamakon rashin yan sanda a titunan Lagas.

Sun tunatar da yan sandan cewa aikinsu shine kare rayuka da dukiyoyin jama’a, inda suka bukaci da su manta da mummunan al’amarin da ya faru a makon da ya gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel