Gwamnati ta fara shari’a da wadanda su ka saci kayan tallafin COVID-19 a Filato

Gwamnati ta fara shari’a da wadanda su ka saci kayan tallafin COVID-19 a Filato

- Gwamnati ta shiga kotu da wadanda ake tuhuma sun saci kayan tallafi a Filato

- Lauyoyi da su ka tsaya wa wadanda ake zargi sun roki Alkalai su yi rangwame

- Kotu ta yanke hukuncin dauri a gidan kurkuku ko tara ga mutanen da aka kama

A ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, 2020, gwamnatin jihar Filato ta fara shari’a da mutanen da ake zargi sun yi sata da tada rikici a kwanakin bayan nan.

Mutane fiye da 300 aka kama da zargin sun saci kayan tallafin COVID-19 da wasu dukiyoyin jama’a, ana kuma zargin wasu da laifin tada zaune-tsaye.

Sauran laifuffukan da ake tuhumar wadannan mutane da su sun hada da haura wa su shiga wurin da ba su da hurumi, tada tarzoma, da damun jama’a.

KU KARANTA: Rufe mutane a gida da yajin aikin ASUU ya jawo ta'adi – Gwamna Bello

Wadanda ake zargin su na tsare a hannun sojoji da ‘yan sanda tun bayan da aka kama su tsakanin ranar Juma’a da Asabar da su ka wuce a Jos da Bukuru.

An gurfanar da wadannan mutane ne daya-bayan-daya a kotu daban-daban a gaban Alkalai masu shari’a N S Dashe, Adar Roseline Baraje, da kuma L B Longs.

Alkali Lawal Sulaiman ya na cikin wadanda su ka fara sauraron wannan kara a ranar Laraba.

A duka karar da Lauyoyin gwamnati su ka shigar, sun bukaci Alkali ya hukunta wadanda aka samu da laifi kamar yadda dokokin kasa da na jihar su ka yi tanadi.

KU KARANTA: Takardun karar Bola Tinubu sun kone kurmus a wajen zanga-zanga

Gwamnati ta fara shari’a da wadanda su ka saci kayan tallafin COVID-19 a Filato
Gwamnan Filato a Aso Villa Hoto: www.pmnewsnigeria.com/2020/10/15/northern-governors-want-reformed-sars-governor-lalong
Asali: UGC

Masu kare wadanda ake tuhuma sun roki Alkalai su yi masu rai. Lauyoyi sun fada wa kotu cewa wannan ne karon farko da aka samu wadanda ake zargi da laifi.

Lauyoyin da su ka tsaya wa wadanda ake zargi sun roki Alkalai su yanke hukunci maras tsauri mai dauke da damar biyan tara tun da sun amsa laifinsu da kansu.

Alkalan sun zartar da hukuncin daurin watanni uku ko su biya N10, 000. Punch ta ce an bada belin da-dama daga cikinsu, za a cigaba da shari’a a ranar Alhamis.

A makwata jihar Kaduna kuma, ƴan sanda sun ce za su ci gaba da bincike har sai sun tabbatar da tabbatar zaman lafiya a duk yankunan da ake tashin-tashina.

Kawo yanzu 'Yan sandan jihar Kaduna sun kama mutum 23, sun karbo babura da aka sace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel