Abin da ya sa Jami’an sojoji za su bayyana dukiyarsu inji Tukur Buratai
- Tukur Yusuf Buratai ya bada umarnin sojoji su rika bayyana kadarori
- Janar Tukur Buratai ya ce hakan zai tabbatar da gaskiyar aikin sojoji
- Shugaban hafsun sojan ya bayyana wannan ne wajen wani taro a jiya
A ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, 2020, Janar Tukur Yusuf Buratai, ya umarci manyan sojojin kasa su bayyana kadarorin da su ka mallaka.
Wannan ya na cikin dokar CCT ta yadda jami’an gwamnati da sauran ma’aikatu za su yi gaskiya.
Da ya ke jawabi a wani taro, shugaban hafsun sojojin kasan ya ce yin hakan zai tabbatar da aiki da gaskiya da kuma yin abin da ya dace a aikinsu.
KU KARANTA: #EndSARS: Lauya ya bukaci Buhari, AGF, IGP, da Buratai su biya N10bn
Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi jawabi wajen taron kara wa juna sani da aka shirya a Abuja domin wayar da kan sojoji a kan dokar CCT.
Ga jawabin na sa:
“Sojojin kasa a karkashin shugabancina, ya na burin tabbatar da aiki da gaskiya, tare da yin abin da ya dace a ko yaushe wajen aiki kamar yadda ya kamata.”
“A dalilin haka na bada umarni a shirya irin wannan taro a duka sassan sojojin kasa a Najeriya.”
KU KARANTA: Jama'a sun koma rokon Jami'an tsaro su koma bakin-aiki
“Na bada umarnin nan ne saboda imani da cewa kowane jami’in soja da aka ba shugabanci ya fahimci muhimmanci bayyana kadarori ga jami’ai.”
Daily Trust ta ce shugaban hukumar CCB, Isa Mohammed, ya yi wa sojojin kasa jawabi a taron ta bakin Farfesa Samuel Ogundare wanda ya wakilce shi.
Babban jam’in sojan kasa, Manjo Janar H. Vintenaba ya tofa albarkacin bakinsa a wajen taron.
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ba za ta amince da satar kayan tallafin COVID-19 ba. Gwamna ya ce zai sa kafar wando da wadanda su ka saci kayan tallafi.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa duk wadanda su ka saci kayan tallafi sai sun yaba wa aya zaki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng