WTO: Kasashe 106 sun yi na’am da tsohuwar Ministar kudi, Okonjo-Iweala
- Kasashe rututu su na goyon bayan Ngozi Okonjo-Iweala a zaben WTO
- Da alamu kasashe fiye da 100 su ka ba takarar Dr. Okonjo-Iweala karfi
- Jamus, Italiya, Faransa, Sifen, su na tare da tsohuwar Ministar Najeriya
Jaridar Punch ta ce wadannan kasashe za su tsaya wa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala wajen ganin ta zama mace ta farko da ta rike shugabancin WTO.
Kasashen Turai da su ke tare da Okonjo-Iweala sun hada da Faransa, Jamus, Austriya, Beljika, Bulgariya, Kuroshiya, Czech, Italiya da kasar Denmak.
KU KARANTA: Dr. Okonjo-Iweala ta sa labule da Shugaba Buhari kan zaben WTO
Sauran kasashen su ne: Saifiros, Estoniya, Finland, Girka, Hungariya, Ireland, Latviya, Lithuaniua, Luxembourg, Malta, Netherlands, da kuma Foland.
Har ila yau har da kasashen Fotugal, Romaniya, Slovakiya, Sloveniya, Sifen, da Siwidin a jerin.
Rahotannin da mu ke samu shi ne kasashe 106 daga cikin 164 da ake da su a kungiyar WTO su na goyon bayan Dr. Okonjo-Iweala ta kawo kujerar.
Haka zalika kungiyar AU ta Afrika mai kasashe 55 ba ta tare da Yoo Myung-hee ta kasar Koriya.
KU KARANTA: An yi waje da wasu masu neman kujerar shugabar WTO
Bayan haka, tsohuwar Ministar Najeriyar ta samu goyon bayan wasu tsirarun kasashen Asiya da kasashen Caribbean da Pacific a takarar da ta ke yi.
AFP ta ce majalisar kasashen Turai ta nuna ta na tare da Okonjo-Iweala. Ana rade-radin cewa yau za a sanar da wanda zai maye gurbin Roberto Azevedo.
Kwanaki kun ji Okonjo-Iweala da Myung Hee sun zarce zuwa matakin zaben karshe a takarar kungiyar WTO da mace ba ta taba zama shugabarta ba.
A halin Dr. Okonjo-Iweala da Ministar kasuwancin Koriya ta Kudu kadai su ka rage a takarar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng