Da ƙyar na sha: DPO ya labarta yadda wasu fusatattun matasa suka so halaka shi a Kubwa
- DPO na ofishin 'yan sanda da ke Kubwa, Abdullahi Bello, ya bayar da labarin yadda arangamarsa ta kasance da wasu bata gari a sansanin NYSC na Kubwa
- Abdullahi Bello ya ce, matasan sun kusa halaka shi, a lokacin da ya ke kokarin hana su fasa babban dakin ajiyar abinci da kayayyaki na sansanin
- DPOn ya ce an ware jami'ai 20 ne don kula da sansanin, amma daga baya aka kara kawo wasu jami'an don tabbatar da doka da oda a wajen
DPO na ofishin 'yan sanda da ke Kubwa, Abdullahi Bello, a ranar Talata ya ce wasu bata gari da suka je yashe sansanin NYSC na Kubwa, sun so caccaka masa wuka yana a bakin aiki.
Mr Bello, wanda bayyana hakan a wata tattauna da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ce sai da shi da mutanensa suka koma gefe, don gudun farmaki daga bata garin.
KARANTA WANNAN: Wanda ya ci ya amayar: Gwamnatin Kaduna ta fara bi gida gida neman kayan COVID-19
Ya ce duk wani kokari na tattaunawa da matasan da zummar yin sulhu, da kuma nusar da su cewa babu kayan tallafi a sansanin, ya zama a bayan kunnen su.
"A lokacin da suka mamaye sansanin bayar da horon a ranar Asabar, munyi magana da su, har muka bude masu dakin ajiyar kayan, basu ga komai na kayan tallafi a ciki ba.
"Amma kwatsam yau muna zaune suka dawo, muka sake yi masu magana, basu saurare mu ba. Su ka fara jifarmu da duwatsu, yayin da wasu suka fara ciro wukake kala kala.
KARANTA WANNAN: Nigeria za ta kai wa Chadi wutar lantarki
"Sula tunkari dakin ajiyar kayan abinci da na amfani da aka tanadawarwa masu shirin yin bautar kasa. Suka kwashe komai, abinci, kayayyaki, kai harma da tsoffin katifu.
"Da kyar na sha, sun so halaka ni ta hanyar yunkurin sossoka mun wuka," a cewar sa, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
DPOn ya ce an ware jami'ai 20 ne don kula da sansanin, amma daga baya aka kara kawo wasu jami'an don tabbatar da doka da oda a wajen.
A wani labarin, Gwamnatin jihar Kaduna ta fara bi gida gida domin gano kayayyakin tallafin COVID-19 da aka sace a dakin ajiyar kayan da ke wasu garuruwa na jihar.
Rundunar 'yan sanda tare da sauran jami'an tsaro ne za su fara wannan atisayen binciken gida gida don gano kayan tare da cafke wadanda aka kama da laifin satar su.
Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya tabbatar da wannan atisayen a shafinsa na Twitter a ranar Talata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng