A Kano: An damke wani Malam Boka yana kokarin kwalkwalewa wani jariri ido don asiri

A Kano: An damke wani Malam Boka yana kokarin kwalkwalewa wani jariri ido don asiri

- Dubun wani boka mai ikirarin malinta ya cika a Hotoron jihar Kano

- Ya sihirce wani matashi wanda yake amfani da shi wajen biyan bukatunsa

- Aikin karshe da ya sa shi shine samo masa sabon jariri domin kwakwale idonsa

Wani Malam Boka a jihar Kano, Yahaya Shehu, ya shiga hannu bayan kokarin cire kwayan idon wani jariri, Ahmad, domin amfani da shi wajen aikin tsubbu.

Wannan abu ya faru a unguwar Hotoro, karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun nuna cewa Bokan ya yi wa wani Kabiru Sani alkawarin N8m da mota idan ya samo masa sabon jariri.

Hukumar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da aukuwan lamarin kuma ta ce tuni an damke Bokan.

Kakakin hukumar, DSP Abdullahi Haruna kwaya, ya ce sun damkeshi ne bayan Kabiru Sani, ya kai kara ofishin yan sanda.

KU KARANTA: Sabbin mutane 119 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 62,111

A Kano: An damke wani Malam Boka yana kokarin kwalkwalewa wani jariri ido don asiri
A Kano: An damke wani Malam Boka yana kokarin kwalkwalewa wani jariri ido don asiri Hoto: Arewa Radio
Asali: Facebook

KU DUBA: Gwamnan Osun ya bai wa masu satar kayan tallafi wa'adi, ya sanar da abinda za su iya fuskanta

"Bayan Sani ya je wajen Bokan domin neman magani, Bokan ya fada masa wani abu da zai gauraya da fitsarinsa kuma yayi wanka dashi na tsawon kwanaki uku," cewar Kakakin yan sanda Kiyawa.

"Komawarsa bayan kwanaki uku, Bokan ya kara masa wani ruwa wanda hakan ya sa shi bin dukkan abinda ya umurcewa, har zuwa ranar da ya umurceshi ya dauka jaririn 'yar uwarsa domin a kwalkwale idonsa na hagu domin amfani."

"Hakan ya sa ya je ya roki yar uwarsa ta kawo jaririnta domin amfani da shi wajen yiwa wani Soja aiki."

"A lokacin ne 'yar uwar ta fahimci halin da ake ciki kuma ta kai Sani ofishin yan sanda inda aka bayyana musu abinda ake ciki,"

Ya kara da cewa ba tara da bata lokaci ba aka damke bokan a Hotoro.

Ya ce an samu abubuwa irinsu makara, kasa, kwarya da wasu rubuce-rubuce a hannunsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel