Abinda yasa karnuka basu yagalgala naman wadanda suka yashe gidana ba - Sanata

Abinda yasa karnuka basu yagalgala naman wadanda suka yashe gidana ba - Sanata

- Dan majalisa mai wakiltar mazabar Oyo ta tsakiya ya ce karnukansa basu yagalgala naman barayin ba

- Ya tabbatar da cewa, karnukan suna cikin keji ne lokacin da matasan mazabarsa suka je suka yashe gidan

- Sanatan ya ce duk baburan da janareton za a raba su ne ga jama'ar mazabarsa da suka shiga suka sace

Teslim Folarin, dan majalisa mai wakiltar mazabar Oyo ta tsakiya, ya ce karnukansa duk suna cikin keji ne, lamarin da yasa basu yagalgala naman wadanda suka kai farmaki gidansa ba a ranar Asabar.

Fiye da babura 250, firji 400, janareto 35 aka kwashe a gidan sanatan wadanda aka ware domin karfafa matasa a mazabarsa.

A tattaunawar da yayi da Dele Momodu a ranar Lahadi, Folarin ya bayyana mamakinsa a kan wannan harin, The Cable ta wallafa.

"Na samu kiran gaggawa cewa wasu bata-gari sun shiga gidana. Na sha mamaki tunda na san babbar kofa garesa. Ina da karnuka amma kuma suna cikin keji a lokacin," ya sanar da Momodu.

“Abu na farko da muka fara shine kiran 'yan sanda amma kuma sun nuna basu son zuwa. Sun ce idan suka je har aka rasa rai, su ne za su shiga matsala.

“Saboda haka ne bamu samu taimako ba. Sun fi karfin masu gadin inda suka shiga gidan, Sun kwashe babura, janarteo da sauransu," yace.

Ya ce yana shirin rarraba kayan ne ga jama'ar yankinsa wadanda suka sace.

KU KARANTA: Yanzu haka: Ana musayar wuta tsakanin mayakan ISWAP da sojoji a Borno

Abinda yasa karnuka basu yagalgala naman wadanda suka yashe gidana ba - Sanata
Abinda yasa karnuka basu yagalgala naman wadanda suka yashe gidana ba - Sanata. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamna ya fatattaki hadimansa na musamman a kan tsaro saboda kona ofisoshin 'yan sanda

A wnai labari na daban, rahotanni sun nuna yadda bata-gari suka saci dukiyoyin gwamnati, ciki har da kayan abincin tallafin COVID-19 a ranar Asabar. An umarci bata-garin wadanda suka yi satar da sunan zanga-zangar EndSARS da su mayar da duk abubuwan da suka sata cikin kwana 3.

Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, yayin da yake zagaye jihar don ganin barnar da suka yi a jiharsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel