‘Yan Sanda sun tabbatar da sace Shugaban karamar hukumar Iganna a Jihar Oyo
- ‘Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma Iganna a jihar Oyo
- An yi garkuwa da Honarabul Olayiwola Adeleke ne a titin Ado Awaye
- A lokacin wannan mutumi da direbansa za su kai ziyara zuwa Ibadan
Rundunar ‘yan sandan Najeriya na jihar Oyo ta tabbatar da sace shugaban karamar hukumar Iganna, Honarabul Olayiwola Adeleke.
A halin yanzu ana kuka da halin rashin tsaro da aka ciki a Najeriya. Sha’anin garkuwa da mutane ya yi kamari, har ana yin gaba da manya.
‘Yan sanda sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da Olayiwola Adeleke ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, 2020, da tsakiyar maraice.
KU KARANTA: Wasu sun yi gigin kona ofishin 'Yan Sanda a Oyo
Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da aukuwar wannan mummunan labari ne a yau Litinin da safe.
Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya bayyana cewa an sace Olayiwola Adeleke ne tare da direbansa.
Fadeyi ya kuma yi karin bayani, ya ce lokacin da wannan abu ya faru, ya na kan hanyarsa ta zuwa garin Ibadan ne ya gana da gwamna.
Daga lokacin da wannan abu ya faru, babu wani labari da aka samu game da bayyanarsa ko kuma tuntubar iyalansa domin su biya kudin fansa.
KU KARANTA: Fafaroma da Mufti Menk sun sa ‘yan Najeriya a addu’a
“Bayanan da su ke zuwa mani ya nuna an sace shi ne a kan titin Ado Aw aye – Iseyin.” Inji jami’in.
Kakakin ‘yan sandan na jihar Oyo ya ce su na kokarin ceto wadannan Bayin Allah. “Mu na kokarin ganin cewa an ceto shi daga hannun miyagu.”
Dazu kun ji cewa wasu Miyagu sun yi garkuwa da Basarake a Kauyen Zamfara. Dakaun ‘Yan Sanda su ka tabbatar da wannan labari a makon jiya.
Hakan na zuwa ne kwanaki da Gwamnan Zamfara ya zauna da Buhari kan lamarin tsaro.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng