Barna: Minista ya bayar da umarnin a kama masu kwasar kayan tallafi, a gurfanar da su

Barna: Minista ya bayar da umarnin a kama masu kwasar kayan tallafi, a gurfanar da su

- Har yanzu wasu fusatattun batagari daga cikin 'yan Najeriya basu daina balle dakunan ajiyar kayan tallafi da gidajen wasu 'yan siyasa ba

- Ko a ranar Litinin sai da Legit.ng ta rawaito cewa wasu mata sun balle wani babban shagon ajiyar kayan abinci da ke Gwagwalada, Abuja

- Ministan babban birnin tarayya, Abuja, ya bukaci jami'an 'yan sanda su kama wadanda suka kwashe kayan cikin shagon tare da gurfanar dasu

Ministan babban birnn tarayya, Abuja, Malam Muhammad Bello, ya bayar da umarnin a kama ma su barnar da suka balle babban shagon kayan abinci da ke unguwar Gwagwalada tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Da tsakara ranar Litinin wasu fusatattun batagarin matasa suka yi dandazo tare da balle babban shagon tare da kwashe dukkan kayan abincin da ke cikinsa.

DUBA WANNAN: Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC

Bello ya bayar da wannan umarni ne yayin taron gaggawa da ya gudanar da shugabannin hukumomin tsaro na Abuja a ranar Litinin.

Barna: Minista ya bayar da umarnin a kama masu kwasar kayan tallafi, a gurfanar da su
Muhammad Bello
Asali: Depositphotos

Ministan ya bukaci mabarnatan su gaggauta dawo da kayan da suka kwashe a yayin da yake sanar da cewa an baza jami'an tsaro domin kare sauran manyan shaguna da ke rukunin masana'antu da ke Idu.

DUBA WANNAN: Tallafin korona: Bidiyon matasa suna balle ma'adanar kayan abinci a Yola

A cewar Bello, abinda ya ke faruwa yanzu ba zanga-zangar ENDSARS ba ce, sata ce da 'yan iskan gari ke yi.

A nata bangaren, karamar ministar Abuja, Dakta Ramatu Aliyu, ta yi Alla-wadai da abinda ya faru cikin kakkausar murya.

Ministar ta ce babu wata kasa da zata rayu ba tare da ma'adanai na abinci ba irin wadanda yanzu mabarnata ke ballewa suna kwashe abincin ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel