Harbin Lekki: Buhari ya magantu, ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya

Harbin Lekki: Buhari ya magantu, ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya

- 'Yan Najeriya sun dade suna jiran martanin shugaba Buhari a kan kashe-kashen da aka yi a Lekki

- A ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, shugaban kasa ya saki wata takarda a kan lamarin

- Ya yi kira ga duk 'yan Najeriya da su zauna lafiya don samun bunkasar arziki

Dangane da matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka a kan kashe-kashen da aka yi a Lekki Toll Gate da ke jihar Legas, mutane da dama sun zauna suna jiran jin ta bakinsa.

A ranar Lahadi, 25 Oktoba ne Shugaban kasar ya saki wata takarda a kan harbin da aka yi a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, wanda hakan ya janyoo rasa rayuka da dama a yankin.

A takardar da hadiminsa a kan harkar labarai, Garba Shehu ya saki, ya ce shugaban kasa ya yi shiru da bakinsa ne don jin gaskiyar labarin yadda al'amura suka faru dalla-dalla.

Shugaban kasa ya nuna alhininsa ga jami'an tsaro da masu zanga-zanga wadanda al'amarin ya shafa, ya kuma tabbatar wa mutanen jihar Legas cewa zai shirya kwamitin bincike wacce zata tabbatar anyi wa kowa adalci.

Shugaban kasa ya yi kira ga 'yan Najeriya da su hada kawunansu don samun kwanciyar hankali da wadatar arziki.

Kwamitin binciken za ta fara aiki ne a ranar Litinin, kuma za'ayi kwatankwacin hakan a sauran jihohi da rikicin ya shafa, Legit.ng ta wallafa.

Shugaba Buhari, ya nuna goyon bayansa a kan taimakon kasa da tabbatar da adalci ga duk masu zanga-zangar lumana da suka rasa rayukansu.

KU KARANTA: Da duminsa: Matasa sun balle gidan Yakubu Dogara, jami'an tsaro sun bude musu wuta

Harbin Lekki: Buhari ya magantu, ya aike muhimmin sako ga wadanda abun ya shafa
Harbin Lekki: Buhari ya magantu, ya aike muhimmin sako ga wadanda abun ya shafa. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun halaka mutum 6 da ake zargin 'yan Boko Haram ne

A wani labari na daban, batagari sun cigaba da yadda suka ga dama da dukiyoyin gwamnati da na al'umma sakamakon barkewar rikicin zanga-zangar EndSARS, Daily Trust ta wallafa.

A jihar Benin, Anambra, Edo, Kaduna, Filato, Cross River da Ekiti, matasa sun yi ta shiga ma'adanai, inda aka ajiye kayan tallafin COVID-19, wadanda ya kamata a raba wa talakawa, suna awon gaba da su.

Manema labarai sun tattaro bayanai a kan yadda mutane 5 suka rasa rayukansu a jihar Edo, 5 a jihar Taraba da kuma wani mutum a Anambra, duk sakamakon kwasar kayan abincin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel