Miyagu sun yi awon gaba da Mai Garin Lingyado da wasu mutane 4

Miyagu sun yi awon gaba da Mai Garin Lingyado da wasu mutane 4

- ‘Yan bindiga sun shiga wani Kauye a jihar Zamfara sun sace mutane 5

- Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da Mai Garin Lingyado

- ‘Yan Sanda sun bayyana cewa su na kokarin gano wadanda aka dauke

Channels TV ta rahoto cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Mai unguwar kauyen Lingyado, a karamar hukumar Maru, a jihar Zamfara.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Zamfara su ka bayyana haka a wani jawabi da ya fito daga kakakinta, Mohammed Shehu a jiya.

Mohammed Shehu ya ce an sace wannan Mai unguwa da wasu mutane hudu a jihar lokacin da ‘yan bindiga su ka auka wa karamar hukumar.

KU KARANTA: Yari ya tonawa Gwamna Matawalle asiri

“A ranar 25 ga watan Oktoba, 2020, da kimanin karfe 8:00, wasu da ake zargin miyagu ne, su ka kawo hari a kauyen Lingyade a karamar hukumar Maru.”

Jawabin jami’an tsaron ya cigaba da cewa: “Su ka yi gaba da Mai unguwa da wasu mutane hudu.”

“An sanar da Dakarun hadin-gwiwa na ‘yan sanda da sojoji da aka kafa a garin Bindin domin gudun irin wannan game da abin da ya faru.”

Ya ce: “Sun yi maza sun garzaya wannan kauyen domin kade fitinar. Zuwansu ya taimaka wajen hana wadannan miyagu garkuwa da mutane rututu.”

KU KARANTA: INEC ta fasa zaben ‘Yan Majalisa a Zamfara dsr saboda #EndSARS

Miyagu sun yi awon gaba da Mai Garin Lingyado da wasu mutane 4
Gwamnan Zamfara da COAS Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Mohammed Shehu ya ce gwamnatin Zamfara ta baza dakarun ‘yan sanda, sojoji da jami’an NSCD 80 a wuraren da ake fama da hatsabiban ‘yan bindiga.

‘Yan sandan su ce jami’an tsaro sun shiga laluben jeji domin kubutar da wadanda aka sace.

A makon da ya gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zauna da gwamnan jihar Zamfara a game da rashin tsaro da ke addabar jihar.

Bello Matawalle ya ce rusa rundunar SARS da IGP ya yi, matsala ce ga al'ummar jiharsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel