Gwamnan Enugu ya nemi afuwar Matasa ya ce #EndSARS ya koya masu darasi

Gwamnan Enugu ya nemi afuwar Matasa ya ce #EndSARS ya koya masu darasi

- David Umahi ya roki Matasa su yi hakuri game da abubuwan da su ka faru

- Gwamnan na Enugu ya nemi afuwar Manyan goben da ya ke jawabi dazu

- Umahi ya ba shugabanni shawara su fara jawo matasan Najeriya tun yanzu

Gwamna David Umahi na jihar Enugu, ya roki matasa da su yafe wa shugabannin Najeriya, ya ce sun dauki izina daga zanga-zanga #EndSARS.

Jaridar Punch ta ce gwamnan ya yi wannan roko ne a lokacin da ya ke yi wa muutanen jihar Enugu bayani a ranar Juma’a, 23 ga watan Oktoba.

David Umahi ya ce ya kamata a san inda aka sa gaba bayan an yi asarar rayuka da tarin dukiyoyi.

KU KARANTA: Abubuwan da jawabin Shugaban kasa a kan #EndSARS su ka taba

Gwamnan ya bukaci matasa su yafe wa harbe-harben ‘na babu gaira babu dalili' da aka yi wa masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki, jihar Legas.

Ya ce: “Mu na yi wa wadanda su ka yi rashi ta’aziyya, mu na kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Legas, ta yi maza ta binciki lamarin (Lekki).”

Umahi ya ce: “Abubuwan more rayuwan da aka lalata a fadin kasar nan, na ku ne, manyan gobe.”

“Dole ku yi rai don ku cin ma gobe saboda wasunku za su zama shugabannin kasa, gwamnoni, ‘yan majalisa da ministoci da sauransu.” Inji Umahi.

KU KARANTA: Matasa su yi wa Gwamna Ortom zanga-zanga, su rabu da #EndSARS

Gwamnan Enugu ya nemi afuwar Matasa ya ce #EndSARS ya koya masu darasi
Gwamnan Enugu Dave Umahi Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

“Babu wanda zai dawwama a Duniya, mu na neman afuwarku domin mu koma ayi sabon lale.”

A jawabinsa, gwamnan ya yi kira ga shugabanni su jawo matasa a jika, su rika cusa su a cikin harkar gwamnati, kasafin kudi, da sauran harkoki.

Dazu mun ji cewa Sultan Abubakar Sa’ad lll ya ce ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amfani da dattaku a lamarin #EndSARS.

Sultan ya bayyana haka ne ta bakin sakataren Kungiyar Jama’atu Nasril Islam na kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng