Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta yi kira a bi a hankali da #EndSARS

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta yi kira a bi a hankali da #EndSARS

- Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta yi jawabi game da zanga-zangar #EndSARS

- Sultan ya bukaci gwamnati ta nuna hikima da dabara wajen kawo zaman lafiya

- Abubakar Sa’ad lll ya yi kira ga mutanen kasa da sojoji su guji harzuka lamarin

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad lll, ta yi magana a game da zanga-zangar #EndSARS da ake yi.

Sultan Abubakar Sa’ad lll wanda shi ne shugaban musulman Najeriya ya soki harin da aka kai wa masu wannan zanga-zanga a jihar Legas.

Abubakar Sa’ad lll ya koka a kan yadda wasu tsageru su ka shiga cikin rigar zanga-zangar lumanar #EndSARS, su na tafka barna iri-iri.

KU KARANTA: #EndSARS: Abin da aka fada wa Gwamna Sanwo-Olu da ya tuntubi Buhari

Mai alfarma Sarkin Musulmai ya zargi tsagerun da kashe mutane da barnata dukiyar al’umma.

Kungiyar ta JNI ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Muhammadu Buhari ya ke jagoranta da sa dattaku da hikima a wajen shawo kan rikicin.

Nasril Islam ta yi wannan jawabi ne ta bakin sakatarenta na kasa, Dr. Khalid Abubakar Aliyu, ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba, 2020 a Kaduna.

Khalid Abubakar Aliyu ya yi wa jawabin da kungiyar ta fitar a jiya take da “Kiran a kwantar da hankali wajen shawo kan dambarwar #EndSARS.”

KU KARANTA: Shugaban kasa zai dauki mataki a kan #EndSARS – NSA

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta yi kira a bi a hankali da #EndSARS
Buhari da Sultan Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

JNI ta ce an fara zanga-zangar bil hakki a dalilin asarar rayukan da SARS su ka jawo, amma a karshe miyagu su ka yi amfani da hakan wajen barna.

Kungiyar ta yi kira ga sojoji da jama’a su guji yin abin da zai jawo tabarbarewar zaman lafiya.

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga matasa su tsagaita zanga-zanga a fadin kasar nan. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana haka a jawabin jiya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa mutanen Najeriya jawabi a ranar Alhamis da yamma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel