EndSARS: Zaben Bayelsa, Legas da sauransu ba yanzu ba Inji Hukumar INEC

EndSARS: Zaben Bayelsa, Legas da sauransu ba yanzu ba Inji Hukumar INEC

- INEC ta ce ta dakatar da gudanar da zabukan da aka shirya a wasu Jihohi 11

- A da an shirya za ayi zaben cike guraben kujerun majalisa a karshen Oktoba

- Dokar kasa ya ba hukumar INEC damar dage zabe idan akwai barazanar tsaro

A sakamakon zanga-zangar #EndSARS da ake ta yi a bangarorin Najeriya, hukumar zabe mai zaman kanta, ta ce ta dakatar da zabukan da aka shirya.

Hukumar INEC ta bada sanarwar cewa ta dage duka zabukan maye gurbi, har sai baba ta gani. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a jiya da dare.

A da INEC ta na da niyyar gudanar da zabukan kujerun majalisar dattawa shida da kuma ‘yan majalisar dokoki tara a wasu jihohin da ke fadin Najeriya.

KU KARANTA: 'Yan iskan gari sun yi ta'adi a ofishin Gwamnan Jihar Ondo

A cewar hukumar, za ta cigaba da sa-idanu ta ga yadda abubuwa su ke kasance wa a duka jihohi da mazabun da za a yi wadannan zabuka na cike gibi.

Bayan haka, INEC za ta zauna da masu ruwa da tsaki wajen harkar zabe, sannan ayi wani zama nan da makonni biyu domin a sa sabon lokacin yin zaben.

Shugaban yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar INEC, Festus Okoye ya bada wannan sanarwa a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, 2020.

Festus Okoye ya fitar da jawabi ne bayan wani taro da aka yi da kwamishinonin zabe 37 a Abuja.

KU KARANTA: An cafke mutane 163 da su ka sulale daga kurkuku

EndSARS: Zaben Bayelsa, Legas da sauransu ba yanzu ba Inji Hukumar INEC
Shugaban Hukumar INEC Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mazabun da za ayi zaben kujerar sanata su ne: Bayelsa ta tsakiya da yamma, Kuros-Riba ta Arewa, Imo ta Arewa Legas ta yamma, sai kuma Filato ta Kudu.

Sai kuma zaben majalisar dokoki da za ayi a Bakura, Ibaji, Kosofe, Obudu, Nganzai da Bayo.

Dazu kuma kun ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta shigar ka karar INEC da kakakin majalisa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila saboda wani kusan hamaya ya koma APC.

Rahotanni sun ce ficewar Honarabul Ephraim Nwuzi daga PDP ta fusata manyan jam'iyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel