Dalilin da yasa muka yi gum da bakinmu a kan harbe-harben Lekki - DHQ

Dalilin da yasa muka yi gum da bakinmu a kan harbe-harben Lekki - DHQ

- A daren ranar Talata ne rahotanni suka wallafa cewa an budewa fararen hula wuta yayin taron gangamin zanga-zanga a yankin Lekki da ke jihar Lagos

- Ana zargin cewa jami'an rundunar soji ne suka kaiwa fararen hular da ke zanga-zanga hari domi tarwatsasu

- A cikin wani jawabi da hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta fitar ranar Alhamis, rundunar soji ta fadi dalilin da yasa har yanzu ta yi shiru a kan lamarin

A ranar Alhamis ne hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana dalilinta na kin cewa uffan dangane da mujadalar harbe-harben da aka yi a yankin Lekki.

A daren ranar Talata ne aka zargi dakarun soji da budewa fararen hula wuta yayin taron gangamin zanga-zanga a yankin Lekki a jihar Lagos domi a tarwatsasu bayan sanar da saka dokar ta baci.

A cewar DHQ, fitar da wani jawabi daga rundunar soji, a halin yanzu, zai iya zama katsalandan ga binciken da gwamnatin jihar Legas ta fara.

A yau, Alhamis, ne gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da cewa gwamnatinsa ta fara bincike a kan harbe-harben Lekki na daren ranar Talata.

KARANTA: Rundunar Soji ta karbe iko da tsaron gidan gwamnatin jihar Imo

Sanwo-Olu ya bayyana cewa gwamnati zata yi amfani da faifan bidiyon da na'urar sa-ido (CCTV) ta nada domin gano gaskiya.

Dalilin da yasa muka yi gum da bakinmu a kan harbe-harben Lekki - DHQ
Manjo Janar John Enenche
Asali: Twitter

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Manjo Janar John Enenche, kakakin DHQ, ya ce har yanzu zargin rundunar soji ake yi.

Janar Enenche ya bukaci 'yan Najeriya su zauna lafiya, su bi doka, su kuma jira sakamakon da kwamitin bincike zai fitar.

KARANTA: Bidiyo: Rundunar soji ta kama sojan da ke goyon bayan ma su zanga-zanga

"Rundunar soji ta na da atisaye kusan guda tara, mu a nan mun fi aiki da manyan atisaye.

"Akwai kananan atisaye irinsu atisayen MENSA wanda jihohi na da iko da shi.

"Bana son shiga cikin batun atisaye, sannan bani da ikon bayyana wasu abubuwan a halin yanzu.

"Muna da hotuna da faifan bidiyo na abubuwan da suka faru, mun gano na karya da ake yadawa daga cikinsu.

"Jama'a su jira sakamakon da kwamitin bincike zai fitar, gaskiya Za ta bayyana, amma yanzu ba zamu ce komai ba saboda hakan zai iya tauye binciken da ake kan yi," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel