Ana ta kamo wasu daga cikin wadanda su ka tsere daga gidajen yari a jihar Edo

Ana ta kamo wasu daga cikin wadanda su ka tsere daga gidajen yari a jihar Edo

- An soma kamo wasu daga cikin wadanda su ka tsere daga gidan yarin Edo

- Jami’an tsaro sun cafke 160, amma ana neman mutum fiye da 1800 har yanzu

- Gwamnan Edo ya sha alwashin cafko ragowar wadanda su ka rage a waje

Hukumomi da jami’an tsaro sun yi dace, an dawo da wasu daga cikin wadanda su ka tsere daga gidajen yari a jihar Edo a cikin makon nan.

Mutane 163 daga cikin wadanda su ka kubce daga wasu gidajen yari biyu a Benin da hanyar Sapele a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, 2020.

Jaridar Leadership ta fitar da rahoto, ta ce mutum 163 daga cikin 1, 993 da su ka fice daga kurkukun sun shiga hannun jami’an tsaro a Edo.

KU KARANTA: Idan aka yi sake karshen #EndSARS ba zai yi kyau ba – Dahiru Bauchi

Hakan na zuwa ne bayan gwamnan Edo Godwin Obaseki ya bada wa’adin kwana biyu ga wadanda su ka yi wannan aiki su koma kurkuku.

Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana cewa muddin lokacin da ya bada ya cika, wadanda su ka balle daga gidan yarin za su ga fushin hukuma.

Obaseki ya gane wa idanunsu abin da ya faru a gidan kurkukun da ke babban birnin jihar Edo, ya sha alwashin kamo wadanda su ka ci kafar kare.

Gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa, Philip Shaibu da wakilin IGP, Johnson Okoye, da shugabannin hukumar gidan kurkuku na jihar Edo.

KU KARANTA: An kona coci da ofishin 'Yan Sanda a Abuja

Ana ta kamo wasu daga cikin wadanda su ka tsere daga gidajen yari a jihar Edo
Gwamnan jihar Edo Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wasu miyagu ne su ka yi sanadiyyar ballewar mutane rututu da ke zaman kaso da jiran shari’a.

Gwamnan ya ce:

“Wannan ba ya cikin zanga-zangar #EndSARS, mummunan laifi ne kawai, wasu tsageru su ka shige cikin rigar zanga-zanga, su ka tsere da abokansu.”

A ranar Laraba ne kuma aka ji cewa 'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, lamarin har ya kai sun yi awon gaba da sandar girmar Mai martaban.

Matasan sun yi barna a fadar, sun bata motoci da abubuwan hawa da wasu dukiya masu daraja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng