COVID-19: Za a gudanar da bincike a kan bacewar N6.2b a NDDC - Majalisa
- ‘Yan Majalisar Tarayya su na binciken zargin awon gaba da kudi a NDDC
- Majalisar Wakilai ta na kuma bibiyar facaka da aka yi a NBET da NIMET
- Babban mai binciken kudin kasa ya na zargin cewa an wawuri wasu kudi
Majalisar wakilan tarayya a Najeriya ta kai ga fara binciken zargin badakala a ma’aikatar NDDC mai kula da cigaban yankin Neja-Delta.
Ana zargin an karkatar da wadannan kudi da aka ware domin bada tallafin COVID-19 a yankin.
KU KARANTA: Masu tada hatsaniya da sunan #EndSARS za su yaba wa aya zaki a Nasarawa
Bayan nan kuma majalisar wakilai ta na kuma binciken barnar Naira biliyan 139.317 da ofishin mai binciken kudi na kasa ya ke ikirari.
Rahoton ya bayyana cewa OAGF ya na zargin an tafka wannan barna ne tsakanin 2013 da 2018.
Sai dai an gamu da cikas wajen binciken, dole ‘yan majalisar su ka dakata da aikinsu a dalilin rashin halartar shugabannin ma’aikatar NDCC.
Sauran wadanda su ka gagara hallara a majalisa wajen wannan bincike sun hada da shugabannin ma’aikatar saida wuta da NIMET.
KU KARANTA: Fatima Ganduje ta na nadamar abu 1 da ta yi a Najeriya
‘Yan majalisar su na kuma bibiyar abin da ma’aikatar Neja-Delta ta yi da kudinta tsakanin Junairun 2018 zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2018.
Hakan ya biyo bayan binciken kudin da gwamnatin tarayya ta yi wanda ta tike a Disamban 2018. An saurari ta bakin jama’a a wajen binciken.
A makon nan ne ku ka ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Oladipo Olusoga Odujinrin a matsayin shugaban NACA.
Olusoga Odujinrin zai rike mukamin shugaban wucin gadi na masu bada shawara a hukumar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng