Obasanjo: Hallaka masu zanga-zangar #EndSARS zai sa a gaza zaman sulhu
- Olusegun Obasanjo ya soki amfani da karfin bindiga wajen maganin zanga-zanga
- Tsohon shugaban ya ce wannan danyen aiki zai kara hura wutan halin da ake ciki
- Obasanjo ya yi kira ga gwamnatin kasar ta yi maza ta dauki mataki kafin a makara
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi tir da amfani da karfi da sojoji su ka yi wajen tasa keyar masu zanga-zanga a Legas.
Cif Olusegun Obasanjo ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba ta dauki duk sauran matakan da ya kamata kafin ta kai ga baza sojoji ba.
KU KARANTA: Gwamnan Legas ya ziyarci 'yan zanga-zanga da aka harbe
Obasanjo ya yi wa jawabin take da: “Statement on Violence Against Protesters In Nigeria: An Appeal for Calm’, ya na kiran a kawo zaman lafiya.
Tsohon shugaban ya gargadi Buhari “a kan amfani da karfin soji da sauran jami’an tsaro wajen yi wa mutane karfa-karfa da nufin shawo kan rikicin.”
Obasanjo wanda ya mulki Najeriya tsakanin 1999 da 2007 ya ce tarihi ya nuna kashe masu zanga-zanga bai kawo kwanciyar hankali, sai ma akasinsa.
Tsohon Janar din ya ce amfani da kan bindiga zai sa a gaza iya zama a kan tebur domin ayi sulhu.
KU KARANTA: Gwamnonin Arewa sun yi gargadi a kan shirya zanga-zanga
A jawabinsa, Obasanjo ya yi kira ga shugaban kasan ya yi maza ya dauki mataki tun kafin abubuwa su yi kamari, a rasa yadda za ayi a fadin kasar.
“An yi ta’adi, amma za a iya shawo kan lamarin kafin ya rincabe gaba daya.” Inji Obasanjo.
Dazu Dahiru Bauchi ya ja-kunnen gwamnati, ya fada mata cewa ba a kashe wuta da wuta, don haka shugaba Buhari ya nemi ya sasanta da masu zanga-zanga.
Shehin malamin ya ce idan aka yi sake karshen zangar-zangar #EndSARS ba zai yi kyau ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng