Daga karshe: Buhari ya magantu kan zanga-zangar #EndSARS, ya roki zaman lafiya

Daga karshe: Buhari ya magantu kan zanga-zangar #EndSARS, ya roki zaman lafiya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan Nigeria musamman masu zanga-zanga da su kwantar da hankalinsu don samar da fahimtar juna

- A cewar Buhari, tuni aka kammala duk wani shiri na yin garambawul a ayyukan rundunar 'yan sandan Nigeria

- Haka zalika, FG ta kafa kotun bincike a jihohin Lagos, Kaduna, Delta, Ekiti, Ogun, Anambra, Enugu, Imo, Plateau, Edo, Nasarawa, Ondo da Akwa Ibom

Fadar shugaban kasa, a ranar Laraba ta roki 'yan Nigeria da su samar da fahimtar juna da kuma hankali a fadin kasar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Fadar shugaban kasar, ta ce tuni aka kammala duk wani shiri na yin garambawul a ayyukan rundunar 'yan sandan Nigeria daga matakin kasa zuwa jihohi.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar, Femi Adesina, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya jaddada kudurin Buhari na yin garmabawul a hukumar kula da rundunar 'yan sandan Nigeria.

KARANTA WANNAN: Bidiyon yadda soji suka ragargaji sansanin horas da mayakan ISWAP a Borno

Daga karshe: Buhari ya magantu kan zanga-zangar #EndSARS, ya roki zaman lafiya
Daga karshe: Buhari ya magantu kan zanga-zangar #EndSARS, ya roki zaman lafiya - @Daily_Trust
Asali: Twitter

Ya ce shugaban kasa Buhari ya amince a samar da kotun bincike a jihohi 13, kamar yadda majalisar tattalin arzikin kasa NEC ta bukata, don binciken ta'addancin 'yan sandan.

Jihohin da aka kafa masu wannan kotun binciken sun hada da: Lagos, Kaduna, Delta, Ekiti, Ogun, Anambra, Enugu, Imo, Plateau, Edo, Nasarawa, Ondo da Akwa Ibom.

Shugaba Buhari wanda ya sha alwashin daukar matakan gaggawa, ya kuma nuna goyon bayansa akan jihohi su tabbatar an kwatarwa kowa hakkinsa kan wannan lamari.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta haramta zanga zanga a fadin jihar Legas

Majalisar NEC, bisa jagorancin Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasa a taron ta na ranar Alhamis 15 ga watan Oktoba, ta yanke shawarar kafa kotun bincike a matakin jihohi.

Kotun za ta yi nazari tare da binciken zarge zargen da ake yiwa 'yan sanda na cin zarafin al'umma, da kuma yankewa ire iren wadanda jami'ai hukunci.

A wani labarin, Kungiyar lauyoyin Nigeria (NBA) ta magantu kan kashe masu zanga zangar @ENDSARS da jami'an rundunar soji suka yi a Lekki Toll Plaza, a daren Talata a jihar Legas.

Rayuka da dama sun salwanta a wannan dare, yayin da hotuna da bidiyoyin da ke yawo a kafofin sada zumunta ke nuna yadda mutane da dama suka jikkata, aka kai su asibitoci daban daban.

Masu zanga zangar na bukatar kawo karshen cin zarafin da 'yan sanda ke yiwa al'umma. Gwamnatin jihar ta sanar da dokar ta baci ta awanni 24 a fadin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng