Kwankwaso @ 64: Abdullahi Ganduje ya taya tsohon Gwamnan Kano murna

Kwankwaso @ 64: Abdullahi Ganduje ya taya tsohon Gwamnan Kano murna

- Abdullahi Ganduje ya tuna da tsohon Mai gidansa yayin da ya kara shekara

- Gwamnan Kano ya taya Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekara 64

- Dr. Ganduje ya yi wa tsohon Gwamna Kwankwaso addu’ar samun nasarori

Gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta taya Rabiu Musa Kwankwaso murnar rana irin ta yau.

A yau, Laraba, 21 ga watan Oktoba, 2020, tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabiu a Kwankwaso ya ke bikin ranar zagayowar haihuwarsa.

Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya shiga cikin sahun mutanen da su ke taya Rabiu Musa Kwankwaso murnar zuwan wannan rana.

KU KARANTA: Rashin gaskiya ta sa Rabiu Kwankwaso ya ajiye aikinsa

Kamar yadda ku ka sani, Sanata Kwankwaso wanda aka haifa a shekarar 1956 ya cika shekara 64.

Kamar yadda mu ka gani, gwamnatin Dr. Umar Ganduje ta taya Kwankwaso murna ne a jaridar Daily Trust, fitowar ranar 21 ga watan yau.

Wannan gaisuwar murna ta zo a shafi na 17 na jaridar, dauke da hoton tsohon gwamnan da jar hula da kuma karamin hoton magajin na sa a kasa.

Sakon ya ce: “A wannan rana ina tuna gwamnatinka da ka yi a mabanbantan lokuta, wanda ina ciki kuma na bada gudumuwa wajen yin ayyuka.”

KU KARANTA: Kano Pillars: Ganduje ya dauko hayar kwararren Bafaranshen koci

Kwankwaso @ 64: Abdullahi Ganduje ya taya tsohon Gwamnan Kano murna
Kwankwaso @ 64 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Yayin da ka kara shekara, ina addu’ar Ubangiji ya cigaba da baka nasarorin kokarin da ka yi.” Inji Ganduje mai shekara 70 a madadin gwamnatinsa.

An haifi ‘dan siyasar ne a Kwankwaso a karamar hukumar Madobi, jihar Kano. Mahaifinsa Musa Saleh, ya na cikin tsofaffin Sarakan kasar Kano.

Idan za ku tuna kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya gina makaranta ta musamman domin makiyaya su samu damar yin karatun boko a Rano.

Tsohon gwamnan ya yi wannan ne a matsayin hanyar murnar kara shekara da ya yi a Duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel