Zangazangar #EndSARS: Ba bu hannuna a cikin harbe-harben da aka yi a Lekki - Tinubu

Zangazangar #EndSARS: Ba bu hannuna a cikin harbe-harben da aka yi a Lekki - Tinubu

- Tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Ahmed Tinubu ya nisanta kansa daga harbe-harbe da aka yi wa masu zanga-zangar EndSARS a yankin Lekki

- Tinubu ya ce ba zai taba bari a hada kai da shi wajen aikata ta'addanci ba

- Jigon na APC ya kuma kara jadadda cewa ba shine ke daukar nauyin zanga-zangar ba kamar yadda ake ta yayatawa

Jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya ce ba zai taba kasance da hannu a cikin kowani irin barna da ta’addanci ba.

Tinubu na martani ne ga harin daren ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, wanda aka gano jami’an tsaro suna bude wuta a kan masu zanga-zangar EndSARS a Lekki da ke Lagas.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya yi magana ne a wata hirar waya da Channels TV a safiyar ranar Laraba, jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya yi watsi da matakin da ake zargin rundunar sojin da dauka, cewa, ta yaya za su yi amfani da harsasai?

KU KARANTA KUMA: Legas: Gwamna Sanwo Olu ya ziyarci wadanda aka harba a Lekki a gadon asibiti

Zangazangar #EndSARS: Ba bu hannuna a cikin harbe-harben da aka yi a Lekki - Tinubu
Zangazangar #EndSARS: Ba bu hannuna a cikin harbe-harben da aka yi a Lekki - Tinubu Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: UGC

“Ba zan taba kasancewa a cikin kowani irin barna ba. Ba zan taba kasancewa da hannu a ciki ba,” in ji shi.

Har ila yau, Tinubu ya kuma karyata batun cewa yana da hannun jari a kamfanin Lekki Concession Company, wacce ke kula da karban kudin shige da ficen ababen hawa a wajen.

“Bani da ko asi, ko kwabo bani da shi da sunan hannun jari a wajen,” in ji shi.

Da yake ci gaba da jawabi, jigon na APC ya ce, “mun shiga kwanaki na 13 zuwa 14 da fara zanga-zangar. Kafin yanzu, an zarge ni an kuma kai karana fadar shugaban kasa cewa nine ke daukar nauyin zanga-zangar.”

Tinubu ya ce ya yi watsi da zargin sannan ya lallashi matasa da Gwamna Babagide Sanwo-Olu a kan ya amshi bukatun masu zanga-zangar.

KU KARANTA KUMA: An tsaurara matakan tsaro a Kaduna yayinda zanga-zanga ke yaduwa

“Wannan ne dalilin da yasa Sanwo-Olu ya kafa kwamitin tuntuba. Gwamnan ya kuma je gidajen wadanda abun ya shafa don basu hakuri.

“Ya tattara naira miliyan 200 don biyan diyyar wadanda aka kai wa hari.”

A gefe guda, mun ji cewa matasan jihar Legas sun afka gidan talabijin TVC News wanda ake zargin mallakin tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel