Legas: Gwamna Sanwo Olu ya ziyarci wadanda aka harba a Lekki a gadon asibiti

Legas: Gwamna Sanwo Olu ya ziyarci wadanda aka harba a Lekki a gadon asibiti

- Gwamnan Legas ya yi maza ya dauki mataki game da kashe-kashen da aka yi

- Mista Babajide Sanwo-Olu ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin takaici

- Gwamna Sanwo-Olu ya yi alkawarin yi wa mutanen Legas jawabi a yau da safe

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya yi maza ya kai ziyara ga wadanda aka buda wa wuta wajen zanga-zangar #EndSARS a Lekki.

Mista Babajide Sanwo-Olu ya yi magana a dandalin Twitter da kimanin karfe 4:00 na safe.

Gwamnan ya kira lamarin abin takaici da bakinciki, ya ce abin ya da auku ya fi karfin ikon gwamnati, ya yi alkawarin yin jawabi a yau da safe.

KU KARANTA: An kama mutanen da su ka kai wa Jagoran 'Yan Sanda hari

“Wannan shi ne daren da ya fi kowane yi mana tsauri a rayuwarmu yayin da wasu su ka kafa mummunan tarihi, amma za mu dawo da karfinmu.”

Mai girma gwamnan ya ke cewa: “Yanzu na kammala kai ziyara a asibitoci, na gana da wadanda wannan mummunan lamari ya auka masu a Lekki.”

Ya ce: “A matsayina na gwamnan jiharmu na fahimci komai zai kare a gaban teburina, zan yi kokarin hada kai da gwamnatin tarayya a shawo kan abin.”

Sanwo-Olu ya kara da cewa zai nemi jami’an tsaro su yi aikinsu na kare rai da dukiyar jama’a.

KU KARANTA: An kona ofishin 'Yan Sanda wajen zanga-zangar #EndSARS

Legas: Gwamna Sanwo Olu ya ziyarci wadanda aka harba a Lekki a gadon asibiti
Gwamna Sanwo Olu Hoto: Twitter/jidesanwoolu
Asali: Twitter

“Zan yi wa mutanen jiha bayani yau da safe.” Yanzu al’ummar jihar Legas sun kasa kunne su na jiran su ji abin da gwamnan zai fada nan ba da da jimawa ba.

Akwai mutane 11 da ke jinya a babban asibitin Legas, 11 a asibitin Reddington, da wasu 4 a Vedic. Kawo yanzu an sallami biyu daga cikin wadanda aka harba.

Dazu kun ji cewa wasu sojojin kasa sun buda wa masu zanga-zanga wuta a yankin Lekki, a dalilin haka sun kashe mutane, wasu kuma su na jinya a asibiti.

Hakan ya jawo irin su Hilary Clinton da Rihana su na tir da kashen-kashen masu zanga-zanga.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng