Hotunan kyawawan gidaje 7 na miliyoyin daloli mallakin Donald Trump

Hotunan kyawawan gidaje 7 na miliyoyin daloli mallakin Donald Trump

- Shugaban kasa Donald Trump babban dan kasuwa ne kuma biloniya ne wanda ya mallaki gidaje a fadin Amurka

- Daga cikin kadarorinsa akwai Trump Tower wacce ke da fadin kafa 10,996 da darajar dala miliyan 54

- Mar-a-Lago wani gidansa ne da ke da dakunan kwana 128 kuma yana wani rukunin gidajensa ne da ke da girman aka 20

Tun kafin shigar shugaba Trump siyasa, ya kasance hamshakin dan kasuwa kuma yana da dukiyar da ta kai dala biliayn 2.5 kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.

Trump shine biloniya na farko da ya taba zama shugaban kasan Amurka. An zabesa a watan Nuwamban 2016 a matsayin shugaban kasar Amurka na 46.

Yana da shekaru 74 kuma yana son zarcewa a kujerarsa a zaben watan Nuwamban 2020.

A wannan rubutun, Legit.ng ta lissafo jerin manyan gidajensa masu matukar tsada da kyau kamar yadda Town and Country Mag ta wallafa.

1. Trump Tower Penthouse, New York City

Wannan yana daya daga cikin katafaran gidajen shugaban kasar Amurakn wanda yake cewa ya kai kafa 33,000. Amma kuma mujallar forbe ta ce kafa 10,996 ne kuma tsadarsa ta kai dala miliyan 54.

Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Asali: Getty Images

2. Mar-a-Lago, Palm Beach

Wannan makeken gidan ana kiransa da "the Winter White House" kuma yana gine ne a kan aka 20. Yana da dakuna 128.

Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Asali: Getty Images

3. Golf Club, Bedminster Township, New Jersey

Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Asali: Instagram

KU KARANTA: Da duminsa: Sojoji da 'yan sanda sun mamaye yankin filin jirgin sama a Abuja

4. Seven Springs, Bedford, New York

Wannan katafaren gidan yana da dakuna 60 daga ciki kuwa 15 duk na bacci ne. Yana da wuraren wanka har 3. Kadarar ta kai darajar dala miliyan 24 kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa.

Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Asali: UGC

5. Trump Winery, Charlottesville, Virginia

Wannan gidan yana gine a kan fili mai girman taku 23,000 kuma yana da dakunan bacci 45.

Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Asali: UGC

6. Le Château des Palmiers, St. Martin

Shugaba Trump ya siya wannan kadarar a 2013 kuma yana amfani da ita ne wurin bada haya. Akwai dakunan bacci 9 da kuma bandakuna 12.

Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Hotunan kyawawan gidajen miliyoyin daloli mallakin Donald Trump
Asali: UGC

7. Donald Trump's Childhood Home in Queens, New York

Wannan gagarumin gidan ne shugaban kasar Amurkan ya girma. Mahaifinsa ne ya gina a 1940. Yana da giraman kafa 2,500 kuma a da ana bada hayarsa ne.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun bayyana matakai 5 da suke dauka a kan EndSARS

A wani labari na daban, a yayin da zaben kasar Amurka na 2020 ke gabatowa, Legit.ng ta tattaro muku jerin motocin alfarma da Shugaba Trump ya mallaka.

A gane cewa, wannan jerin motocin an bayyana su a 2017 ne, akwai yuwuwar an kara wasu a kai. An gano cewa, a 2015 shugaban kasa Trump ya ce arzikinsa ya kai dala biliyan 10.

Amma kuma wani rahoton mujalla Fobes bayan shekaru biyu ya nuna cewa arzikinsa ya karye inda ya koma dala biliyan 3.7.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel