Jihohi biyar da aka sanar da saka dokar hana fita saboda zanga-zanga

Jihohi biyar da aka sanar da saka dokar hana fita saboda zanga-zanga

- Zangar-zangar lumana da aka fara domin nuna adawa da rundunar SARS ta rikide zuwa rikici a wasu jihohin Nigeria da Abuja

- Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin baza jami'an kwantar da tarzoma a fadin kasa

- Ya zuwa yanzu gwamnatocin wasu jihohi biyar sun sanar da kakaba dokar ta baci domin shawo kan zanga-zangar

Tuni zanga-zangar lumana da aka fara domin nuna adawa da rundunar SARS ta rikide zuwa kazamin rikici a wasu jihohi da kuma birnin tarayya, Abuja.

Legit.ng Hausa ta wallafa cewa gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya kafa dokar hana fita ta awa 24 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu sakamakon ballewar rikici na zanga-zangar EndSARS a jihar.

Da ya ke yin jawabi a yammacin ranar Talata, gwamnan ya ce dokar hana fitar za ta fara aiki daga karfe 8 na dare har zuwa wani lokaci nan gaba.

KARANTA: An samu AK47 guda 5, an kama mutane 12 bayan ma su zanga-zanga sun kone ofishin 'yan sanda a Benin

Kafin jihar Plateu, Jihar Legas ta sanar da cewa sakamakon sauyawar salon zanga-zanga wcce ta haifar da kashe-kashe da kone-kone, gwamnatin jihar ta saka dokar ta baci a dukkan sassan jihar.

Jihohi biyar da aka sanar da saka dokar hana fita saboda zanga-zanga
Jami'an 'yan sanda
Asali: UGC

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita, ranar Talata.

Ya baiwa mutanen jihar daman komawa gidajensu zuwa karfe 4 na yamma saboda daga lokacin ''ba a son ganin kowa a waje."

Gwamnatin jihar Edo ce ta fara sanar da sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a fadin jihar.

Dokar za ta fara aiki daga karfe 4:00pm na ranar 19 ga watan Oktoba, har sai baba-ta-gani.

KARANTA: Daya daga cikin matasan da ke jagorantar zanga-zanga ya janye hannunsa, ya bayyana dalilinsa

Babban sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie, ne ya fitar da sanarwar da Channels TV ta ruwaito.

Ogie ya bayyana cewa an sanya takunkumin ne sakamakon hare-haren da wasu yan iska da suka mamaye zanga-zangar #ENDSARS suka aiwatar.

Biyo bayan kashe wani dan sanda tare da guduwa da makamansa da wasu matasa fiye da 30 suka yi a jihar Abia, gwamna Okezie Ikpeazu, ya saka dokar hana fita ta tsawon sa'a 24.

Kwamishian yada labarai na jihar Abia, John Okiyi Kalu, ne ya sanar da hakan a daren ranar Talata.

Jiha ta biyar da aka sanar da saka dokar hana fita ta tsawon sa'a 24 ita ce jihar Ekiti.

Gwamnan jihar, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta saka dokar ne bayan nazari a kan batagari suka fara fakewa da zanga-zangar ENDSARS wajen tafka barna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel