EndSARS: Ba zan sa hannu a kasafin badi ba sai za a biya diyya – Gbajabiamila
- Shugaban majalisar wakilan tarayya ya yi magana kan zanga-zangar #EndSARS
- Femi Gbajabiamila ya ce dole a biya diyyar wadanda ‘Yan Sanda su ka ci wa zarafi
- Sai an duba bukatun kungiyar ASUU sannan majalisa za ta amince da kasafin 2021
Shugaban majalisar wakilan tarayya ya sha alwashin kin amincewa da kundin kasafin kudin badi muddin bai kunshe da bukatun kungiyar ASUU.
Femi Gbajabiamila ya kuma bayyana cewa majalisar wakilai ba za ta yi na’am da kasafin kudin shekarar 2021 sai an ware kudin diyyar #EndSARS.
KU KARANTA: #EndSARS: NCS ba ta san yawan wadanda su ka kubuce daga kurkuku ba
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya nuna zai tashi tsayin-daka wajen gannin gwamnati ta biya hakkin wadanda dakarun SARS su ka ci wa zarafi a Najeriya.
“Ku matasa da ke zanga-zanga kun zaburar da kasa wajen daukar mataki… Mun ga bukatunku, ka da ku bari wasu tsageru su shige-gaban gwagwarmayarku.”
Ya ce: “Ka da ku bari wasu su zuga ku, ku ki janye zanga-zangar da ku ke yi da sunan an ji kunya.”
Haka zalika majalisar tarayya za ta kare hakkin malaman jami’a da ke faman yajin-aiki a kasar. ASUU ta na kukan gwamnati ta yi watsi da harkar ilmi.
KU KARANTA: Magoya-bayan Buhari za su shirya zanga-zangar lumana
Ya ja-kunnen matasan cewa: “Akwai miyagun da su ke ganin damar cusa munanan muradunsu a cikin tafiyarku, su raba-kan jama’a, su durkusa kasa”
Game da bukatun kungiyar ASUU, kakakin majalisa ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta sake duba kudin da ake ware wa sha’anin ilmi a Najeriya.
Dazu kun ji cewa ganin yadda zanga-zangar #EndSARS ta yi kamari, Sanatoci sun kira zaman musamman a majalisar dattawa a safiyar ranar Talata.
Bayan haka an sake samun Jihar da ta rufe makarantun boko saboda masu zanga-zangar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng