Anzo wajen: Zanga-zangar #EndSARS ta sauya zani, ta koma ta'addanci a Filato

Anzo wajen: Zanga-zangar #EndSARS ta sauya zani, ta koma ta'addanci a Filato

- Gangamin #EndSARS a Jos, jihar Filato, ya zama rikici bayan yan iska sun karbe zanga-zangar da ake cikin lumana

- An tattaro cewa harkokin kasuwanci sun tsaya yayinda aka lalata motoci da shugana masu yawa

- Sai dai, an tura yan sanda yankin da abun ya faru domin dawo da zaman lafiya

Wani zanga-zangar #EndSARS da ake gudanarwa a garin Jos, babbar birnin jihar Filato, ya kaure ya zama rikici, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton, an samu tashin hankali a hanyar Ahmadu Bello Way da ke garin Jos yayinda masu zanga-zanga suka sanya shingaye a babban titin da ke sada mutum da cikin birnin a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba.

A kan haka, wasu matasa sun samu sabani da wadanda suka sanya shingen, wanda hakan ya haifar da tashin hankali. An farfasa motoci da yawa sannan aka kona wasu, an kuma lalata shaguna.

An tattaro cewa an rufe harkoki a birnin domin hana ci gaban barnar.

KU KARANTA KUMA: Legas: 'Yan daba sun banka wa sakatariya wuta, anyi sace-sace

Anzo wajen: Zanga-zangar #EndSARS ta sauya zani, ta koma ta'addanci a Filato
Anzo wajen: Zanga-zangar #EndSARS ta sauya zani, ta koma ta'addanci a Filato Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

An kuma jiyo karar harbe-harben bindiga a yankin, lamarin da ya tursasa mazauna yankin barin wajen. A halin yanzu, an turo jami’an tsaro domin kwantar da tarzoman.

A bangaren The Nation kuma, ta ruwaito cewa Zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS da SWAT a Jos ya koma rikici a ranar Talata, sakamakon mamaye wajen da yan iska suka yi sannan suka farfasa motoci da kona su.

Rahoton ya kara da cewar yan iskan sun kai wa mutane hari tare da sace-sace.

KU KARANTA KUMA: Sabuwar zanga zanga ta barke a Abuja: An kashe mutum daya, da yawa sun jikkata

A gefe guda, wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kona ofishin 'yan sanda da ke karamar hukumar Ifelodun na jihar Legas.

Wasu da lamarin ya faru a gabansu sun tabbatar wa The Punch afkuwar abin a ranar Talata.

Tunda farko, wasu da ake kyautata zaton bata garin ne sun kona ofishin yan sanda da ke Orile Iganmu duk dai a jihar ta Legas.

Lamarin ya faru ne misalin karfe 9.45 na safiya kamar yadda wadanda abin ya faru a gabansu suka bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng