Buhari na da ‘ya’ya, ya san yadda halin matasa yake – Obasanjo ya yi magana kan #Endsars a karon farko

Buhari na da ‘ya’ya, ya san yadda halin matasa yake – Obasanjo ya yi magana kan #Endsars a karon farko

- Karo na farko, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasonjo ya yi martani kan zanga-zangar #EndSARS

- Obasanjo ya ce ya kamata shugaba Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa game da lamarin ta hanyar biyan bukatun masu zanga-zangar

- Tsohon shugaban kasar ya ce zanga-zangar da matasan ke yi ba komai bane face son samun rayuwa mai inganci da nagarta

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna kulawarsa ga matasa ta hanyar biya masu bukatunsu.

Obasanjo ya yi magana ne a lokaccin da ya ziyarci Adeyeye Ogunwusi, Ooni na Ife, a fadarsa da ke Ile-Ife, jihar Osun, a ranar Litinin.

Ya bayyana zanga-zangar #EndSARS a masayin wata babbar fafutuka da matasan Najeriya ke yi, jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yan Kudu na zanga zanga ne don ƙwace mulki daga Arewa a 2023 - Miyetti Allah

Buhari na da ‘ya’ya, ya san yanda halin matasa yake – Obasanjo ya yi magana kan #Endsars a karon farko
Buhari na da ‘ya’ya, ya san yanda halin matasa yake – Obasanjo ya yi magana kan #Endsars a karon farko Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

Ya ce matasan na fafutukar ne domin samun ingantaccen rayuwa sannan akwai hanyoyi da dama da gwamnati za ta iya bi don nuna cewa ta fahimci damuwarsu ta hanyar saukaka masu abubuwa.

“Fiye da kaso 65 cikin 100 na yawanmu sun fada a tsakanin shekaru 18 da 30; ba wai kawai suna fafutuka don saun ilimi bane, suna son samun rayuwa mai inganci,” in ji Obasanjo.

“Wasu daga cikinsu basu samu ilimi ba, yayinda wadanda suka yi karatu kuma sun fara gajiya saboda ba su sau damammaki ba. Ya zama dole a kamo bakin zaren.

“Amma ina ganin cewa akwai wasu damammaki da gwamnati za ta fito da su domin nuna cewa ta damu da jin dadin al’umma, musamman matasa, a matsayinta na uban kasa, kuma a matsayinsa na uban matasa.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: An kona ofishin 'yan sanda a Legas

“Abun farin ciki, Shugaban kasar na da ‘ya’ya kuma ya san yadda halin matasa yake. Ina ganin cewa ana iya amfani da damar a sanar da matasan cewa, a matsayinsa na uba, ya fahimci damuwarsu kuma gwamnatinsa ta fahimci damuwarsu kuma a shirye yake da ya inganta rayuwarsu," ya kara da cewa.

A gefe guda, Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ) Bola Tinubu ya shiga sahun masu kira ga matasa su tsagaita zanga-zangar #ENDSARS da suka fara kimanin makonni biyu yanzu.

Ya yi kira ga matasa su daina inda yace."Kun bayyana abubuwan da kuke so kuma gwamnati ta yi muku alkawari. Ku taimaka ku daina zanga-zangan kuma ku ba gwamnati damar aiwatar da bukatunku."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel