Yan Kudu na zanga zanga ne don ƙwace mulki daga Arewa a 2023 - Miyetti Allah

Yan Kudu na zanga zanga ne don ƙwace mulki daga Arewa a 2023 - Miyetti Allah

- Kungiyar makiyaya na Miyetti Allah Kautal Hore, ta zargi Tinubu da sauran yan siyasan kudu da daukar nauyin zanga-zangar #EndSARS

- Kungiyar ta yi zargin cewa an shirya zanga-zangar ne domin dagula gwamnatin Buhari da kuma tsorata arewa ta yadda ba za ta nemi shugabancin kasa ba bayan 2023

- Sai dai kuma Tinubu ya yi watsi da zargin a wata sanarwa da kakakinsa ya yi

Wata kungiyar makiyaya, Miyetti Allah Kautal Hore, ta zargi tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Tinubu, da daukar nauyin zanga-zangar #EndSARS.

Matasan Najeriya ne suka shirya zanga-zangar inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta soke rundunar yan sandan SARS saboda barnar da mambobinta ke aikatawa.

Matasan sun kuma yi kira ga yin garambawul a tsarin yan sanda gaba daya da kuma biyan diyya ga wadanda aka ci zali.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Yan ta'adda sun kaiwa jami'an ƴan sandan RRS hari a Lagos

Zanga-zangar EndSARS shiri ne don hana arewa mulki har bayan 2023, Miyetti Allah ya yi ikirari
Zanga-zangar EndSARS shiri ne don hana arewa mulki har bayan 2023, Miyetti Allah ya yi ikirari Hoto: @daily_trust/@nigeriantribune
Asali: Twitter

Yayinda gwamnatin Najeriya ta rushe rundunar SARS, masu zanga-zangar sun jero sauran bukatunsu da ba a biya ba tukuna.

Sai dai kuma, Miyetti Allah, a wani rahoto daga jaridar The Sun ta yi ikirarin cewa wasu yan siyasa daga yankin kudancin kasar, ciki harda Tinubu, sune ke daukar nauyin zanga-zangar fadin kasar.

Kungiyar ta yi zargin cewa shirin domin dagulawa da tunkude gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da kuma son tsoratar da arewa don ta hakura da yancinta na jagoranci har bayan 2023.

Legit.ng ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi dauke da sa hannun sakataren kungiyar, Alhaji Bello Bodejo da Alhasan Saleh.

KU KARANTA KUA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun harba wa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa a Abuja

Kungiyar ta dasa ayar tambaya kan dalilin da zai sa matasa su ci gaba da zanga-zanga da tayar da rigima bayan an cika burinsu na soke SARS.

Sai dai, Tunde Rahman, mai magana da yawun Bola Tinubu, yace babu gaskiya a zantukan da ke yawo na cewa yana daga cikin wadanda suka dau nauyin zanga-zangar EndSARS.

A wata takarda da ya fitar a ranar Asabar, Rahman ya ce Tinubu ba zai iya daukar nauyin zanga-zangar da za ta shafi tattalin arzikin jihar Legas ba.

Ya kara da cewa, ba zai yuwu jigo a jam'iyyar APC ya dauka nauyin zanga-zangar ba a duk jihohin da take faruwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel