Hukuma ta ce wasu sun fice daga gidan maza a dalilin zanga-zangar #EndSARS

Hukuma ta ce wasu sun fice daga gidan maza a dalilin zanga-zangar #EndSARS

- NCS ta ce ta soma binciken ballewa da aka yi daga gidan yarin Garin Benin

- Hukumar ta ce har yanzu ba ta da adadin wadanda su ka balle a ranar Litinin

- Ana ta yin Allah-wadai da danyen aikin da wasu bata-gari su ka yi a jihar Edo

Kawo yanzu, hukumomi a Najeriya ba su da adadin masu zaman kaso da su ka tsere daga gidan kurkukun Benin, jihar Edo, a makon nan.

A ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, 2020, wasu bata-gari su ka aukawa gidan yarin Benin, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa wasu da ke tsare.

Hukumar NCS mai kula da kurkuku a Najeriya ta yi jawabi a ranar Litinin, bayan abin ya auku, ta ce ta na bincike domin tantance wadanda su ka balle.

KU KARANTA: Magoya-bayan Buhari za su nunawa ‘Yan #EndSARS yadda ake yin zanga-zanga

NCS ta fitar da jawabi ne ta bakin kakakinta, Austin Njoku, ya ce hukumar ta na bincike domin a iya tabbatar da yawan wadanda su ka tsere jiya.

Austin Njoku ya tabbatar da harin da aka kai, ya ce: “An kai wa gidan kurkuku farmaki da safen nan, da sunan zanga-zangar #EndSARS a Benin.”

“Ana kokarin cin karfin lamarin, a shawo kan bin da ta faru a gidajen yarin. Gandurobobi su na fadi-tashi na ganin abubuwa sun dawo daidai.”

Njoku ya yi kaca-kaca da wadanda su ka shirya wannan zanga-zanga, ya ce ba ta lumana ba ce, ya ce sun jawo hatsaniya, sun tada hankalin jama’a.

KU KARANTA: Tarihin Janar Yakubu Gowon yayin da ya cika shekara 85 yau a Duniya

Hukuma ta ce wasu sun fice daga gidan maza a dalilin zanga-zangar #EndSARS
Ministan cikin gida Hoto: www.adabanijaglobal.com.ng/resume-ogbeni-rauf-adesoji-aregbesola
Asali: UGC

Har zuwa lokacin da ya yi jawabi, NCS ba ta san adadin ‘yan gidan kurkukun da yanzu su ke waje ba.

A jiya kun ji cewa bata-gari sun yi yunkurin kutsawa gidan kurkuku na biyu a Jihar Edo. ‘Yan iska sun tasa Garin Benin a gaba, sun kona ofishin wani ‘Yan Sanda.

Duk da dokar ta-baci da aka sa a jiya, ‘Yan iskan gari sun kai hari a ofishin ‘Yan Sanda a Benin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel