Ya isa haka, ku sassauta - Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zanga

Ya isa haka, ku sassauta - Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zanga

- Daga karshe, manyan yan siyasa sun fara magana kan zanga-zangarn #ENDSARS

- Ranar Litinin wasu yan baranda sun kona ofishin yan sanda kuma sun fasa gidajen yari biyu a Edo

- Hakazalika a Osun, wasu da suka cakude cikin yan zanga-zanga sun kaiwa gwamnan hari

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ) Bola Tinubu ya shiga sahun masu kira ga matasa su tsagaita zanga-zangar #ENDSARS da suka fara kimanin makonni biyu yanzu.

Ya yi kira ga matasa su daina inda yace. "Kun bayyana abubuwan da kuke so kuma gwamnati ta yi muku alkawari. Ku taimaka ku daina zanga-zangan kuma ku ba gwamnati damar aiwatar da bukatunku."

A jawabin da ya rattafa hannunsa kuma ya daura a shafinsa na Tuwita, Tinubu ya ce yan Najeriya, musamman matasa na da hakkin fitowa su bayyana abubuwan da basu so.

Ya jaddada cewa babu laifi don sun bukaci a gyara hukumar yan sanda.

Amma ya bukaci masu zanga-zangan su gudanar da kansu bisa dokokin kasa, kuma yayi gargadin kada suyi abinda zai saba doka.

Jagoran na APC ya ce zanga-zangar za ta zama dama ga jam'iyyarsa ta yi dubi cikin abubuwan da ya kamata a gyara.

KU KARANTA: Jami’in Banki ya fadawa Alkali kudin da aka zuba a asusu a karar Fayose v EFCC

Ya isa haka, ku sassauta - Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zanga
Ya isa haka, ku sassauta - Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zanga Hoto: TVC
Asali: UGC

KU KARANTA: Nan da makonni biyu daruruwan yan Najeriya zasu kamu da Korona - Gwamnatin tarayya

Gabanin yanzu, Tunde Rahman, mai magana da yawun Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC, yace babu gaskiya a zantukan da ke yawo na cewa yana daga cikin wadanda suka dauka nauyin zanga-zangar EndSARS.

A wata takarda da ya fitar a ranar Asabar, Rahman ya ce Tinubu ba zai iya daukar nauyin zanga-zangar da za ta shafi tattalin arzikin jihar Legas ba.

Ya kara da cewa, ba zai yuwu jigo a jam'iyyar APC ya dauka nauyin zanga-zangar ba a duk jihohin da take faruwa.

"Akwai bukatar a yi bayani tare da gane cewa wannan labarin bogi ne wanda wasu suka kirkiro," Rahman yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel