Ni ba matar yara ba ce, ta manya ce — Jaruma Rashida Maisa’a

Ni ba matar yara ba ce, ta manya ce — Jaruma Rashida Maisa’a

- Jarumar Kannywood, Rashida maisa'a ta mayar da martani ga saurayin da ya nuna ra'ayin aurenta

- Rashida ta yi masa hannunka mai sanda, inda tace ita ta sha miya don haka matar manya ce ba wai ta kananan yara ba

- Matashin dai da fari ya wallafa wasu zantukan bege da shaukin son jarumar

Shahararriyar jaruman nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Rashida Abdullahi Maisa’a ta bayyana cewa ita ba matar yara bace, saboda haka yara su kiyayi cewa suna nemanta da aure.

Jarumar ta fadi hakan ne a yayinda take mayar da martani ga furucin da wani matashi ya yi na cewa zai aure ta.

A kwanaki ne wani saurayi mai suna Musa Rafinkuka ya wallafa hotunan jarumar tare da rubuta zantukan soyayya a shafinsa na Facebook cewa yana son jarumar.

Ya wallafa cewa gimbiya sarautar mata da za ta amince to da ya yi wuf da ita kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Ni ba matar yara ba ce ta manya ce — Jaruma Rashida Maisa’a
Ni ba matar yara ba ce ta manya ce — Jaruma Rashida Maisa’a Hoto: rashidamaisaa
Asali: Twitter

An tattaro cewa kwana daya da fadin haka, matashin ya yi faifan bidiyo inda ya janye maganarsa tare da neman afuwar jarumar a kan kalaman da ya yi cewa yana son ta da aure.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Ƴan majalisa suna shirin haramtawa kotu korar shugaban ƙasa da gwamnoni

Matashin ya kara da cewa babu wanda ya yi masa barazana har ya fitar da faifan bidiyon.

“Maganar gaskiya babu wani mutum da ya yi mini barazana a kan abin da na yi.

“Da muka yi magana a waya ta nuna min bacin ranta.

“Nasiha kawai ta yi min cewa abin da na yi bai dace ba don haka na ga dacewar a nemi afuwarta ta wannan hanya da na bi na yi mata wannan abu,” in ji shi.

A nata bangaren, Rashida Mai sa’a ta bayyana cewa bayan da matashin ya yi wancan bayani sun yi magana da shi a waya inda ta nuna masa cewa ruwa ba sa’an kwando ba ne.

“Mun yi magana da shi wannan matashi wanda ya shaida min cewa ya kasance yana son fina-finaina tun yana karami.

“Ya rasa ta yadda zai yi sakonsa ya isa gare ni shi ya sa ya yi wannan magana.

“Na fada masa cewa abin da ya yi bai kyauta ba.

“Babu abin da na gaya masa; na dai gaya masa cewa ni ba yarinya ba ce, na kwana biyu.

“Ni matar manya ce ba ta yara ba. Ka kalli Maisa’a mana,” in ji ta.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Buhari ya kori shugaban hukumar hakkin mallaka

A wani labarin, Shahararren jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Ali Nuhu, ya lashe amansa inda a yanzu ya shiga sahun masu zanga-zangar neman a tsare arewa.

Da farko dai Ali ya ki shiga cikin zanga-zangar bisa wasu dalilai nasa na kansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel