Kungiyoyi su na tare da manyan Arewa kan korar su Janar Buratai, Siddique
- Wasu kungiyoyi masu zaman kansu 23 sun koka a kan rashin tsaro
- Wadannan kungiyoyi sun yi tir da halin da ake ciki a yankin Arewa
- Kungiyoyin su na so ayi waje da shugabannin tsaro, a nada matasa
Wata gamayya ta kungiyoyi 23 masu zaman kansu, sun nuna goyon-baya ga kiran da wasu dattawan Arewa su ke yi kan matsalar rashin tsaro.
Wadannan kungiyoyi sun caccaki irinsu Campaign Against Impunity, wadanda ba su goyon bayan a sauya shugabannin tsaron da ke ofis tun 2015.
Jaridar Vanguard ta ce kungiyoyin nan masu zaman kansu, sun yi Allah-wadai da ra’ayin Campaign Against Impunity mai adawa da wannan kira.
KU KARANTA: Jega da wasu manya sun ba Buhari shawarar tsige Hafsun soji
A ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba, wadannan kungiyoyi su ka fitar da jawabi, su ka ce mafi yawan jama’a su na goyon bayan tsige hafsoshin.
Wadanda su ka sa hannu a wannan jawabi su ne: M. Dan Dutse na Actions Against Terrorism, Ibrahim Bichi na kungiyar for Change Agent Initiative.
Sai Mazi Anayo Orji daga Igbo League of Professionals (ILEP), Hajiya Hazida Mohammed ta Northern Children Rights Advocacy Group (NOCHRAG).
Sauran kungiyoyin su ne OPN, BOPAF, ZAPESEA da Action Against Violation of Children Africa.
KU KARANTA: Aisha Buhari ta bukaci a kawo karshen rashin tsaro
A cewar wadannan kungiyoyi da wasunsu, sauke hafsun sojojin daga mukamansu zai taimaka wajen gyara sha’anin tsaro da ya tabarbare a halin yanzu.
Su ka ce a yau babu zaman lafiya a yankin Arewa don haka a maye gurbinsu da masu jini a jika.
A baya kun ji cewa Kungiyar Northern Elders for Peace and Development ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi maza ya cansa hafsun sojoji.
Dattawan yankin Arewan sun yi Allah-wadai da rashin tsaro da ake fama da shi a mulkin APC.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng