Da ɗuminsa: Gwamnatin Edo ta sanya dokar ta ɓaci ta awanni 24 a fadin jihar
- Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya saka dokar hana fita na sa’o’i 24
- Wannan mataki ya biyo bayan harin da wasu yan iska suka aiwatar a safiyar yau Litinin
- Gwamnatin ta Edo ta kuma bayyana cewa dokar za ta fara aiki daga karfe 4:00 na rana
Gwamnatin jihar Edo ta sanar da sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a fadin jihar.
Dokar za ta fara aiki daga karfe 4:00pm na ranar 19 ga watan Oktoba, har sai baba-ta-gani.
Babban sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie ne ya fitar da sanarwar, Channels TV ta ruwaito.
Ogie ya bayyana cewa an sanya takunkumin ne sakamakon hare-haren da wasu yan iska da suka mamaye zanga-zangar #ENDSARS suka aiwatar.
KU KARANTA KUMA: Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja
“Akwai bukatar daukar wannan mataki saboda lamarin barna da hare-hare da yan iska wadanda suka fake da zanga-zangar #ENDSARS suka kai kan mutane.
“Yayinda gwamnatin jihar Edo ke mutunta yancin al’ummanta na gudanar da zanga-zangar lumana, ba za ta zauna ta zuba ido tana kallon yan iska su dauki doka a hannunsu ba domin haifar da rikici a kan al’umman da basu ji ba basu gani ba da jihar,” in ji Ogie.
An bukaci makarantu da wuraren kasuwanci su rufe harkokinsu bayan sanarwar.
KU KARANTA KUMA: Ruth Inomina: Mutumiyar Neja-Delta ta samu shiga Sojan ruwan USMV
An shawarci mutane da su dakatar da zirga-zirga daga yanzu zuwa 4:00pm har sai an dawo da zaman lafiya.
Wasu yan iska a safiyar ranar Litinin sun mamaye sanya-zangar kawo karshen rundunar SARS a birnin Benin.
Babban mai bayar da shawara ga Godwin Obaseki a kafofin watsa labarai, Crusoe Osagie, ya fada ma Channels TV cewa yan iskan sun yi musayar wuta da jami’an tsaro a wani kurkuku da ke birnin Benin.
“A yanzu haka, yan iskan na musayar wuta da jami’an tsaro a Oko, birnin Benin,” in ji.
A baya mun ji cewa dumbin mazauna wani gidan yari da ke birnin Benin a jihar Edo sun samu damar tserewa bayan wasu batagari da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun balle gidan yarin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng